المعارج   سورة  : Al-Ma'aarij


سورة Sura   المعارج   Al-Ma'aarij
يُبَصَّرُونَهُمْ ۚ يَوَدُّ الْمُجْرِمُ لَوْ يَفْتَدِي مِنْ عَذَابِ يَوْمِئِذٍ بِبَنِيهِ (11) وَصَاحِبَتِهِ وَأَخِيهِ (12) وَفَصِيلَتِهِ الَّتِي تُؤْوِيهِ (13) وَمَن فِي الْأَرْضِ جَمِيعًا ثُمَّ يُنجِيهِ (14) كَلَّا ۖ إِنَّهَا لَظَىٰ (15) نَزَّاعَةً لِّلشَّوَىٰ (16) تَدْعُو مَنْ أَدْبَرَ وَتَوَلَّىٰ (17) وَجَمَعَ فَأَوْعَىٰ (18) ۞ إِنَّ الْإِنسَانَ خُلِقَ هَلُوعًا (19) إِذَا مَسَّهُ الشَّرُّ جَزُوعًا (20) وَإِذَا مَسَّهُ الْخَيْرُ مَنُوعًا (21) إِلَّا الْمُصَلِّينَ (22) الَّذِينَ هُمْ عَلَىٰ صَلَاتِهِمْ دَائِمُونَ (23) وَالَّذِينَ فِي أَمْوَالِهِمْ حَقٌّ مَّعْلُومٌ (24) لِّلسَّائِلِ وَالْمَحْرُومِ (25) وَالَّذِينَ يُصَدِّقُونَ بِيَوْمِ الدِّينِ (26) وَالَّذِينَ هُم مِّنْ عَذَابِ رَبِّهِم مُّشْفِقُونَ (27) إِنَّ عَذَابَ رَبِّهِمْ غَيْرُ مَأْمُونٍ (28) وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ (29) إِلَّا عَلَىٰ أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ (30) فَمَنِ ابْتَغَىٰ وَرَاءَ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْعَادُونَ (31) وَالَّذِينَ هُمْ لِأَمَانَاتِهِمْ وَعَهْدِهِمْ رَاعُونَ (32) وَالَّذِينَ هُم بِشَهَادَاتِهِمْ قَائِمُونَ (33) وَالَّذِينَ هُمْ عَلَىٰ صَلَاتِهِمْ يُحَافِظُونَ (34) أُولَٰئِكَ فِي جَنَّاتٍ مُّكْرَمُونَ (35) فَمَالِ الَّذِينَ كَفَرُوا قِبَلَكَ مُهْطِعِينَ (36) عَنِ الْيَمِينِ وَعَنِ الشِّمَالِ عِزِينَ (37) أَيَطْمَعُ كُلُّ امْرِئٍ مِّنْهُمْ أَن يُدْخَلَ جَنَّةَ نَعِيمٍ (38) كَلَّا ۖ إِنَّا خَلَقْنَاهُم مِّمَّا يَعْلَمُونَ (39)
الصفحة Page 569
(11) Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa,
(12) Da matarsa da ɗan'uwansa.
(13) Da danginsa, mãsu tattarã shi.
(14) Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi.
(15) A'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã,
(16) Mai twãle fãtar goshi.
(17) Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai.
(18) Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka.
(19) Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi.
(20) Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri.
(21) Kuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa.
(22) Sai mãsu yin salla,
(23) Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne.
(24) Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne.
(25) Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon.
(26) Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako.
(27) Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro.
(28) Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce.
(29) Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne.
(30) Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne.
(31) To, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka.
(32) Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.
(33) Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne.
(34) Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne.
(35) Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne
(36) Mẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu).
(37) Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a!
(38) Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba)?
(39) A'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022