(77) Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa, "Ka yi tafiyar dare da bãyiNa. Sa'an nan ka dõka musu hanya a cikin tẽku tana ƙẽƙasasshiya, bã ka tsõron riskuwa, kuma bã ka fargabar nutsẽwa."
(78) Sai Fir'auna ya bi su game da rundunarsa. Sai abin da ya rufe su daga tẽku ya rufe su.
(79) Kuma Fir'auna ya ɓatar da mutãnensa, kuma bai shiryar (dasu) ba.
(80) Yã Banĩ Isrã'ĩla! Lalle Mun tsẽrar da ku daga maƙiyinku, kuma mun yi muku wa'adi a gẽfen Dũtsen nan na dãma, kuma Mun sassaukar da darɓa da tattabaru dõminku.
(81) Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurtã ku kuma kada ku ƙẽtare haddi a cikinsa har hushĩNa ya sauka a kanku. Kuma wanda hushĩNa ya sauka a kansa, to, lalle ne, ya fãɗi.
(82) Kuma lalle Nĩ haƙĩƙa Mai gãfara ne ga wanda ya tũba kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai, sa'an nan kuma ya nẽmi shiryuwa.
(83) "Kuma mẽne ne ya gaggautar da kai ga barin mutãnenka? Yã Mũsã!"
(84) Ya ce: "Su ne waɗannan a kan sãwũna, kuma na yi gaggãwa zuwa gare Ka, yã Ubangiji! Dõmin Ka yarda."
(85) Ya ce: "To, lalle ne, haƙĩƙa, Mun fitini, mutãnenka daga bayãnka, kuma sãmiri ya ɓatar da su."
(86) Sai Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa yanã mai hushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Yã mutãnẽna! shin, Ubangijinku bai yi muku wa'adi ba, wa'adi mai kyau? Shin, lõkacin ya yi tsãwo a kanku ne, kõ kun yi nufi ne wani hushi ya sauka a kanku daga Ubangijinku, sabõda haka kuka sãɓã wa alkawarĩna?"
(87) Suka ce: "Ba mu sãɓa wa alkawarinka ba da ĩkonmu kuma amma an ɗõra mana waɗansu kãya masu nauyi daga abin ƙawar mutãnen ne, sai muka jẽfar da su. Sa'an nan kamar haka ne sãmiri ya jẽfa."