التغابن   سورة  : At-Taghaabun


سورة Sura   التغابن   At-Taghaabun
التغابن At-Taghaabun
يُسَبِّحُ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۖ لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ (1) هُوَ الَّذِي خَلَقَكُمْ فَمِنكُمْ كَافِرٌ وَمِنكُم مُّؤْمِنٌ ۚ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ (2) خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ بِالْحَقِّ وَصَوَّرَكُمْ فَأَحْسَنَ صُوَرَكُمْ ۖ وَإِلَيْهِ الْمَصِيرُ (3) يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَيَعْلَمُ مَا تُسِرُّونَ وَمَا تُعْلِنُونَ ۚ وَاللَّهُ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ (4) أَلَمْ يَأْتِكُمْ نَبَأُ الَّذِينَ كَفَرُوا مِن قَبْلُ فَذَاقُوا وَبَالَ أَمْرِهِمْ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ (5) ذَٰلِكَ بِأَنَّهُ كَانَت تَّأْتِيهِمْ رُسُلُهُم بِالْبَيِّنَاتِ فَقَالُوا أَبَشَرٌ يَهْدُونَنَا فَكَفَرُوا وَتَوَلَّوا ۚ وَّاسْتَغْنَى اللَّهُ ۚ وَاللَّهُ غَنِيٌّ حَمِيدٌ (6) زَعَمَ الَّذِينَ كَفَرُوا أَن لَّن يُبْعَثُوا ۚ قُلْ بَلَىٰ وَرَبِّي لَتُبْعَثُنَّ ثُمَّ لَتُنَبَّؤُنَّ بِمَا عَمِلْتُمْ ۚ وَذَٰلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرٌ (7) فَآمِنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ وَالنُّورِ الَّذِي أَنزَلْنَا ۚ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ (8) يَوْمَ يَجْمَعُكُمْ لِيَوْمِ الْجَمْعِ ۖ ذَٰلِكَ يَوْمُ التَّغَابُنِ ۗ وَمَن يُؤْمِن بِاللَّهِ وَيَعْمَلْ صَالِحًا يُكَفِّرْ عَنْهُ سَيِّئَاتِهِ وَيُدْخِلْهُ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ۚ ذَٰلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ (9)
الصفحة Page 556
التغابن At-Taghaabun
(1) Abin da yake a cikin sammai da wanda yake a cikin ƙasã sunã tasbĩhi ga Allah. Gare Shi mulki yake, kuma gare Shi gõdiya take. Kuma Shi, a kan kõme, Mai ikon yi ne.
(2) Shĩ ne wanda Ya halitta ku. Sa'an nan daga gare ku akwai kãfiri kuma daga gare ku akwai mũmini. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.
(3) Ya halitta sammai da ƙasã da abin da yake hakkinSa. Kuma Ya sũranta ku, sa'an nan Ya kyautata sũrõrinku. Kuma zuwa gare Shi makõma take.
(4) Yanã sanin abin da ke a cikin sammai da ƙasã. Kuma Yanã sanin abin da kuke bõyẽwa da abin da kuke bayyanãwa. Kuma Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza.
(5) Shin, babban lãbãri bai je muku ba na waɗanda suka kãfirta daga gabãni, sai suka ɗanɗani uƙũbar al'amarinsu kuma sunã da wata azãba mai raɗaɗi?
(6) Wancan sabõda lalle su Manzanninsu sun kasance sunã jẽ musu da hujjõji bayyanannu, sai suka ce: "Ashe, wasu mutane za su shiryar da mũ?" Sai suka kãfirta kuma suka jũya bãya, kuma Allah Ya wadãtu (daga gare su). Kuma Allah wadãtacce ne, Gõdadde.
(7) Waɗanda suka kãfirta sun riya cẽwa bã zã a tãyar da su ba. Ka ce: "Ni, inã rantsuwa da Ubangijĩna. Lalle zã a tãyar da ku haƙĩƙatan, sa'an nan kuma lalle anã bã ku lãbãri game da abin da kuka aikata. Kuma wannan ga Allah mai sauƙi ne."
(8) Sabõda haka ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa da hasken nan da Muka saukar. Kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Mai labartawa ne.
(9) A rãnar da Yake tattara ku dõmin rãnar tãruwa. Wancan ne rãnar kãmunga. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah, kuma ya aikata aikin ƙwarai, zai kankare masa mũnãnan ayyukansa, kuma Yashigar da shi gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu har abada. Wannan ne babban rabo mai girma.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022