(54) "Bã mu cẽwa, sai dai kurum sashen abũbuwan bautawarmu ya sãme ka da cũtar hauka." Yace: "Lalle ne nĩ, inã shaida waAllah, kuma ku yi shaidar cẽwa" lalle ne nĩ mai barranta ne dagb abin da kuke yin shirki da shi."
(55) "Baicin Allah: Sai ku yi mini kaidi gabã ɗaya, sa'an nan kuma kada ku yi mini jinkiri."
(56) "Haƙĩƙa, ni na dõgara ga Allah, Ubangijĩna kuma Ubangijinku. Bãbu wata dabba fãce Shi ne Mai riko ga kwarkwaɗarta. Haƙĩƙa, Ubangijĩna Yanã (kan) tafarki madaidaici."
(57) "To! Idan kun jũya, haƙĩƙa, nã iyar muku abin da aka aiko ni da shi zuwa gare ku. Kuma Ubangijĩna Yanã musanya waɗansu mutãne, waɗansunku su maye muku. Kuma bã ku cũtar Sa da kõme. Lalle Ubangijina a kan dukkan kõme, Matsari ne."
(58) Kuma a lõkacin da umurninmu ya je, Muka kuɓutar da Hũdu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sabõdawata rahama daga gare Mu. Kuma Muka kuɓutr da su daga azãba mai kauri.
(59) Haka Ãdãwa suka kasance, sun yi musun ãyõyin Ubangijinsu, kuma sun sãɓa wa ManzanninSa, kuma sun bi umurnin dukan mai girman kai, makangari.
(60) Kuma an biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyada Rãnar Kiyãma. To! Lalle ne Ãdãwa sun kãfirta da Ubangijinsu. To, Nĩsa ya tabbata ga Ãdãwa, mutãnen Hũdu!
(61) Kuma zuwa ga Samũdãwa (an aika) ɗan'uwansu Sãlihu. Ya ce: "Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa fãce Shi. Shĩ ne Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma Ya sanya ku mãsu yin kyarkyara a cikinta. Sai ku nẽme Shi gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare Shi. Lalle Ubangijina Makusanci ne Mai karɓãwa."
(62) Suka ce: "Ya Sãlihu! Haƙĩƙa, kã kasance a cikinmu, wanda ake fatan wani alhẽri da shi a gabãnin wannan. Shin kana hana mu bauta wa abin da ubanninmu suke bauta wa? Kuma haƙĩƙa mũ, munã cikin shakka daga abin da kake kiran mu gare shi, mai sanya kõkanto."