القصص   سورة  : Al-Qasas


سورة Sura   القصص   Al-Qasas
فَلَمَّا جَاءَهُم مُّوسَىٰ بِآيَاتِنَا بَيِّنَاتٍ قَالُوا مَا هَٰذَا إِلَّا سِحْرٌ مُّفْتَرًى وَمَا سَمِعْنَا بِهَٰذَا فِي آبَائِنَا الْأَوَّلِينَ (36) وَقَالَ مُوسَىٰ رَبِّي أَعْلَمُ بِمَن جَاءَ بِالْهُدَىٰ مِنْ عِندِهِ وَمَن تَكُونُ لَهُ عَاقِبَةُ الدَّارِ ۖ إِنَّهُ لَا يُفْلِحُ الظَّالِمُونَ (37) وَقَالَ فِرْعَوْنُ يَا أَيُّهَا الْمَلَأُ مَا عَلِمْتُ لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرِي فَأَوْقِدْ لِي يَا هَامَانُ عَلَى الطِّينِ فَاجْعَل لِّي صَرْحًا لَّعَلِّي أَطَّلِعُ إِلَىٰ إِلَٰهِ مُوسَىٰ وَإِنِّي لَأَظُنُّهُ مِنَ الْكَاذِبِينَ (38) وَاسْتَكْبَرَ هُوَ وَجُنُودُهُ فِي الْأَرْضِ بِغَيْرِ الْحَقِّ وَظَنُّوا أَنَّهُمْ إِلَيْنَا لَا يُرْجَعُونَ (39) فَأَخَذْنَاهُ وَجُنُودَهُ فَنَبَذْنَاهُمْ فِي الْيَمِّ ۖ فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الظَّالِمِينَ (40) وَجَعَلْنَاهُمْ أَئِمَّةً يَدْعُونَ إِلَى النَّارِ ۖ وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ لَا يُنصَرُونَ (41) وَأَتْبَعْنَاهُمْ فِي هَٰذِهِ الدُّنْيَا لَعْنَةً ۖ وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ هُم مِّنَ الْمَقْبُوحِينَ (42) وَلَقَدْ آتَيْنَا مُوسَى الْكِتَابَ مِن بَعْدِ مَا أَهْلَكْنَا الْقُرُونَ الْأُولَىٰ بَصَائِرَ لِلنَّاسِ وَهُدًى وَرَحْمَةً لَّعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ (43)
الصفحة Page 390
(36) To, a lõkacin da Mũsã ya jẽ musu da ãyõyinMu bayyanannu, suka ce: "Wannan ba kõme ba sai sihiri, wanda aka ƙãga, kuma ba mu ji wannan ba daga wajen ubanninmu na farko."
(37) Kuma Mũsã ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sanin wanda ya zo da shiriya daga gare Shi, da wanda ãƙibar gida take kasancẽwa agare shi. Lalle ne mãsu zãlunci bã su cin nasara."
(38) Kuma Fir'auna ya ce: "Yã ku mashãwarta! Ban san kunã da wani abin bautãwa baicina ba, sabõda haka ka hũra mini wuta, ya Hãmãnu! a kan lãka (dõmin a yi tũbali), sa'an nan ka sanya mini bẽne tsammãnĩna zan ninƙãya zuwa ga Ubangijin Mũsã kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, inã zaton sa daga maƙaryata."
(39) Kuma ya kangare, shi da rundunõninsa a cikin ƙasa, bã da haƙƙi ba kuma suka zaci cẽwa sũ, bã zã a mayar da su zuwa gare Mu ba.
(40) Sai Muka kãma shi, shĩ da rundunõninsa sai Muka jẽfa su a cikin kõgi. Sai ka dũbi yaddaãƙibar azzãlumai ta kasance.
(41) Kuma Muka sanya su shũgabanni, sunã kira zuwa ga wuta, kuma a Rãnar ¡iyãma bã zã a taimake su ba.
(42) Kuma Muka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyakuma a Rãnar ¡iyãma sunã daga waɗanda aka mũnana halittarsu.
(43) Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã Littãfi daga bãyan Mun halakar da ƙarnõnin farko, dõmin su zama abũbuwan kula ga mutãne, da shiriya da rahama, tsammãninsu sunã tunãwa.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022