الليل   سورة  : Al-Lail


سورة Sura   الليل   Al-Lail
الشمس Ash-Shams
وَالشَّمْسِ وَضُحَاهَا (1) وَالْقَمَرِ إِذَا تَلَاهَا (2) وَالنَّهَارِ إِذَا جَلَّاهَا (3) وَاللَّيْلِ إِذَا يَغْشَاهَا (4) وَالسَّمَاءِ وَمَا بَنَاهَا (5) وَالْأَرْضِ وَمَا طَحَاهَا (6) وَنَفْسٍ وَمَا سَوَّاهَا (7) فَأَلْهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَقْوَاهَا (8) قَدْ أَفْلَحَ مَن زَكَّاهَا (9) وَقَدْ خَابَ مَن دَسَّاهَا (10) كَذَّبَتْ ثَمُودُ بِطَغْوَاهَا (11) إِذِ انبَعَثَ أَشْقَاهَا (12) فَقَالَ لَهُمْ رَسُولُ اللَّهِ نَاقَةَ اللَّهِ وَسُقْيَاهَا (13) فَكَذَّبُوهُ فَعَقَرُوهَا فَدَمْدَمَ عَلَيْهِمْ رَبُّهُم بِذَنبِهِمْ فَسَوَّاهَا (14) وَلَا يَخَافُ عُقْبَاهَا (15)
الليل Al-Lail
وَاللَّيْلِ إِذَا يَغْشَىٰ (1) وَالنَّهَارِ إِذَا تَجَلَّىٰ (2) وَمَا خَلَقَ الذَّكَرَ وَالْأُنثَىٰ (3) إِنَّ سَعْيَكُمْ لَشَتَّىٰ (4) فَأَمَّا مَنْ أَعْطَىٰ وَاتَّقَىٰ (5) وَصَدَّقَ بِالْحُسْنَىٰ (6) فَسَنُيَسِّرُهُ لِلْيُسْرَىٰ (7) وَأَمَّا مَن بَخِلَ وَاسْتَغْنَىٰ (8) وَكَذَّبَ بِالْحُسْنَىٰ (9) فَسَنُيَسِّرُهُ لِلْعُسْرَىٰ (10) وَمَا يُغْنِي عَنْهُ مَالُهُ إِذَا تَرَدَّىٰ (11) إِنَّ عَلَيْنَا لَلْهُدَىٰ (12) وَإِنَّ لَنَا لَلْآخِرَةَ وَالْأُولَىٰ (13) فَأَنذَرْتُكُمْ نَارًا تَلَظَّىٰ (14)
الصفحة Page 595
الشمس Ash-Shams
(1) Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta.
(2) Kuma da wata idan ya bi ta.
(3) Da yini a lõkacin da ya bayyana ta.
(4) Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta.
(5) Da sama da abin da ya gina ta.
(6) Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta.
(7) Da rai da abin da ya daidaita shi.
(8) Sa'an nan ya sanar da shi fãjircinsa da shiryuwarsa.
(9) Lalle ne wanda ya tsarkake shi (rai) ya sãmi babban rabo.
(10) Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe shi (da laifi) ya tãɓe.
(11) Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu.
(12) A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu).
(13) Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!"
(14) Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi).
(15) Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar).
الليل Al-Lail
(1) Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa.
(2) Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa.
(3) Da abin da ya halitta namiji da mace.
(4) Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke.
(5) To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa.
(6) Kuma ya gaskata kalma mai kyãwo.
(7) To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi.
(8) Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa.
(9) Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo.
(10) To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani.
(11) Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta).
(12) Lãlle aikinMu ne, Mu bayyana shiriya.
(13) Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne.
(14) Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022