(12) Sai Ya hukunta su sammai bakwai a cikin kwãnuka biyu. Kuma Ya yi wahayi, a cikin kõwace sama da al'amarinta, kuma Muka kãwata sama ta kusa da fitilu kuma don tsari. Wancan ƙaddarãwar Mabuwãyi ne, Masani.
(13) To, idan sun bijire sai ka ce: "Nã yi muku gargaɗi ga wata tsãwa kamar irin tsãwar Ãdãwa da samũdãwa."
(14) A lõkacin da Manzanninsu suka je musu daga gaba gare su kuma daga bãyansu, "Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah." suka ce: "Dã UbangiJinmu Yã so, lalle dã Ya saukar da malã' iku, sabõda haka lalle mũ, mãsu kafirta ne a game da abin da aka aiko ku da shi."
(15) To, amma Ãdãwa, sai suka yi girman kai a cikin kasã, bã da wani hakki ba, suka ce: "Wãne ne mafi tsananin ƙarfi daga gare mu?" Ashe, kuma ba su gani ba cẽwa Allah, wanda Ya halitta su Shĩne Mafi ƙarfi daga gare su, kuma sun kasance a game da ãyõyinMu suna yin musu?
(16) Sai Muka aika, a kansu, da iska mai tsananin sauti da sanyi, a cikin kwãnuka na shu'umci, dõmin Mu ɗanɗana musu azãbar wulãƙanci, a cikin rãyuwar dũniya, kuma lalle azãbar Lãhira ita ce mafi wulãƙantarwa, kuma sũ bã zã a taimake su ba.
(17) Kuma amma Samũdãwa, sai Muka shiryar da su, sai suka fi son makanta a kan shiriya, dõmin haka tsawar azãbar wulãkanci, ta kamã su sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa (dõmin nẽman wata fã'ida).
(18) Kuma Muka tsĩrar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka kasance sunã yin taƙawa.
(19) Kuma rãnar da ake tãra maƙiyan Allah zuwa wutã, to, sũ anã kakkange su.
(20) Har idan sun jẽ mata, sai jinsu da ganinsu da fãtunsu, su yi shaida a kansu a game da abin da suka kasance sunã aikatawa.