(131) Sa'an nan idan wani alhẽri ya jẽ musu, sai su ce: "Masĩfa ta sãme su, sai su yi shu'umci da Mũsã da wanda yake tãre da shi, To, shu'umcinsu a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawansu bã su sani!"
(132) Kuma suka ce: "Kõ me ka zõ mana da shi daga ãyã, dõmin ka sihirce mu da ita, to, baza mu zama, sabõda kai, mãsu ĩmãni ba."
(133) Sai Muka aika a kansu da cikõwa, da fãra, da ƙwarƙwata da kwãɗi, da jini; ãyõyi abũbuwan rarrabẽwa; Sai suka kangare, kuma suka kasance mutãne mãsu laifi.
(134) Kuma a lõkacin da masĩfa ta auku a kansu, sukan ce: "Yã Mũsã! Ka rõƙa mana Ubangijinka, sabõda abin da Ya yi alkwari a wurinka, lalle ne idan ka kau da azãbar daga barinmu, haƙĩƙa Munã ĩmãni sabõda kai, kuma munã sakin Banĩ Isrã'ila tĩre da kai."
(135) To, a lõkacin da Muka kuranye azãba daga barinsu zuwa a wani ajali wanda suke mãsu iske shi ne, sai gã su sunã warwarẽwa!
(136) Sai Muka yi azãbar rãmuwa, daga gare su, sabõda haka Muka nutsar da su a cikin tẽku, dõmin lalle ne sũ, sun ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma sun kasance daga barinsu, gãfilai.
(137) Kuma Muka gãdar da mutãnen, waɗanda sun kasance anã raunana su, a gabacin ƙasa da yammacinta, wadda Muka sanya albarka a cikinta, kuma kalmar Ubangijinka mai kyau ta cika a kan Banĩ Isrã'ĩla, sabõda abin dasuka yi na haƙuri. Kuma Muka murtsuke abin da Fir'auna da mutãnensa suka kasance sunã sanã'antawa, da abin da suka kasance sunã shimfiɗãwa.