(80) Kõ kã nẽma musu gãfara ko ba ka nẽma musu ba, idan ka nẽma musu gãfara sau saba'in, to, Allah bã zai gãfarta musu ba. Sabõda sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne fãsiƙai.
(81) Waɗanda aka bari sun yi farin ciki da zamansu a bãyan Manzon Allah, kuma suka ƙi su yi jihãdi da dũkiyõyinsu da rãyukansu a cikin hanyar Allah, kuma suka ce: "Kada ku fita zuwa yãƙi a cikin zãfi."Ka ce: "Wutar Jahannama ce mafi tsanlnin zãfi." Dã sun kasance sunã fahimta!
(82) Sabõda haka su yi dãriya kaɗan, kuma su yi kũkada yawa a kan sãkamako ga abin da suka kasance sunã tsirfatãwa.
(83) To, idan Allah Ya mayar da kai zuwa ga wata ƙungiyã daga gare su sa'an nan suka nẽme ka izni dõmin su fita, to, ka ce: "Bã zã ku fita tãre da nĩ ba har abada, kuma bã zã ku yi yãƙi tãre da nĩ ba a kan wani maƙiyi. Lalle ne kũ, kun yarda da zama a farkon lõkaci, sai ku zauna tãre da mãtã mãsu zaman gida."
(84) Kuma kada ka yi salla a kan kõwa daga cikinsu wanda ya mutu, har abada, kuma kada ka tsaya a kan kabarinsa. Lalle ne sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa, kuma sun mutu alhãli kuwa sunã fãsiƙai.
(85) Kuma kada dũkiyõyinsu da ɗiyansu su bã ka sha'awa. Abin sani kawai, Allah Yanã nufin Ya yi musu azãba da su a cikin dũniya, kuma rãyukansu su fita alhãli kuwa sunã kãfirai.
(86) Kuma idan aka saukar da wata sũra cẽwa; Ku yi ĩmãni da Allah kuma ku yi jihãdi tãre da ManzionSa. Sai mawadãta daga gare su su nẽmi izninka, kuma su ce: Ka bar mu mu kasance tãre da mazauna.