الروم   سورة  : Ar-Room


سورة Sura   الروم   Ar-Room
وَعْدَ اللَّهِ ۖ لَا يُخْلِفُ اللَّهُ وَعْدَهُ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ (6) يَعْلَمُونَ ظَاهِرًا مِّنَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَهُمْ عَنِ الْآخِرَةِ هُمْ غَافِلُونَ (7) أَوَلَمْ يَتَفَكَّرُوا فِي أَنفُسِهِم ۗ مَّا خَلَقَ اللَّهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا إِلَّا بِالْحَقِّ وَأَجَلٍ مُّسَمًّى ۗ وَإِنَّ كَثِيرًا مِّنَ النَّاسِ بِلِقَاءِ رَبِّهِمْ لَكَافِرُونَ (8) أَوَلَمْ يَسِيرُوا فِي الْأَرْضِ فَيَنظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ كَانُوا أَشَدَّ مِنْهُمْ قُوَّةً وَأَثَارُوا الْأَرْضَ وَعَمَرُوهَا أَكْثَرَ مِمَّا عَمَرُوهَا وَجَاءَتْهُمْ رُسُلُهُم بِالْبَيِّنَاتِ ۖ فَمَا كَانَ اللَّهُ لِيَظْلِمَهُمْ وَلَٰكِن كَانُوا أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ (9) ثُمَّ كَانَ عَاقِبَةَ الَّذِينَ أَسَاءُوا السُّوأَىٰ أَن كَذَّبُوا بِآيَاتِ اللَّهِ وَكَانُوا بِهَا يَسْتَهْزِئُونَ (10) اللَّهُ يَبْدَأُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُ ثُمَّ إِلَيْهِ تُرْجَعُونَ (11) وَيَوْمَ تَقُومُ السَّاعَةُ يُبْلِسُ الْمُجْرِمُونَ (12) وَلَمْ يَكُن لَّهُم مِّن شُرَكَائِهِمْ شُفَعَاءُ وَكَانُوا بِشُرَكَائِهِمْ كَافِرِينَ (13) وَيَوْمَ تَقُومُ السَّاعَةُ يَوْمَئِذٍ يَتَفَرَّقُونَ (14) فَأَمَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فَهُمْ فِي رَوْضَةٍ يُحْبَرُونَ (15)
الصفحة Page 405
(6) Wa'adin Allah, Allah bã ya sãɓãwa ga wa'adinsa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
(7) Sunã sanin bayyanannar rãyuwar dũniya, alhãli kuwa sũ shagalallu ne daga rãyuwar Lãhira.
(8) Shin, ba su yi tunãni ba a cikin zukãtansu cẽwa Allah bai halitta sammai da ƙasa ba da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya da ajali ambatacce? Kuma lalle mãsu yawa daga mutãne kãfirai ne ga gamuwa da Ubangijinsu?
(9) Shin, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã dõmin su gani yadda aƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Sun kasance mafiya ƙarfi daga gare su kuma suka nõmi ƙasa suka rãya ta fiye da yadda suka raya ta, kuma manzanninsu suka je musu da hujjoji bayyanannu. Sabo da haka Allah ba Ya yiwuwa Ya zãlunce su, amma kansu suka kasance sunã zãlunta.
(10) Sa'an nan ãƙibar waɗannan da suka aikata mũgun aiki ta kasance mafi muni, wãtau sun ƙaryata game da ãyõyin Allah, kuma suka kasance sunã izgili da su.
(11) Allah ne ke fãra yin halitta, sa'an nan Ya sãke ta sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku.
(12) Kuma a rãnar da sa'a ke tsayuwa, mãsu laifi zã su kãsa magana.
(13) Kuma bã su da mãsu cẽto daga abũbuwan shirkinsu, kuma snn kasance mãsu kãfircẽwadaga abũbuwan shirkinsu.
(14) Kuma a rãnar da Sa'a ke tsayuwa, a rãnar nan mutãne ke farraba.
(15) To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai to sũ anã faranta musu rãyuka, a cikin wani lambu.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022