(87) Allah bãbu abin bautawa face Shi. Lalle ne haƙĩƙa Yana tãra ku har zuwa ga Yinin ¡iyãma bãbu shakka a cikinsa. Kuma wãne ne mafi gaskiya daga Allah ga 1ãbãri.
(88) To, mẽne ne ya sãme ku a cikin munãfukai kun zama ƙungiya biyu, alhãli kuwa Allah ne Ya mayar da su sabõda abin da suka tsirfanta? Shin, kunã nufin ku shiryar da wanda Allah Ya ɓatar ne? Kuma wanda Allah Ya ɓatar to bã zã ka sãmi wata hanya ba zuwa gare shi.
(89) Suna gũrin ku kãfirta kamar yadda suka kãfirta, dõmin ku kasance daidai. Sabõda haka kada ku riƙi wasu masõya daga cikinsu, sai sun yõ hijira a cikin hanyar Allah. Sa'an nan idan sun jũya, to, ku kãmã su kuma ku kashe su inda duk kuka sãme su. Kuma kada ku riƙi wani masõyi daga gare su ko wani mataimaki.
(90) Fãce dai waɗanda suke sãduwa zuwa ga wasu mutãne waɗanda a tsakãninku da su akwai alkawari, kõ kuwa waɗanda suke sun je muku (domin) ƙirãzansu sun yi ƙunci ga su yãke ku, kõ su yãƙi mutãnensu. Kuma dã Allah Yã so lalle ne, dã Yã bã su ĩko a kanku, sa'an nan, haƙĩka, su yãke ku. To, idan sun nĩsance ku sa'an nan ba su yãƙe ku ba, kuma suka jẽfa sulhu zuwa gare ku, to, Allah bai sanya wata hanya ba, a gare ku, a kansu.
(91) Za ku sãmi wasu sunã nufin su amintar da ku kuma su amintar da mutãnensu, kõ da yaushe aka mayar da su ga fitina, sai a dulmuyã su a cikinta. To, idan ba su nĩsance ku ba, kuma sun jẽfa sulhu zuwa gare ku, kuma sun kange hannuwansu, to, ku kãmã su, kuma ku kashe su inda duk kuka kãmã su, kuma waɗannan, Mun sanya muku dalĩli bayyanannea kansu.