التوبة   سورة  : At-Tawba


سورة Sura   التوبة   At-Tawba
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا قَاتِلُوا الَّذِينَ يَلُونَكُم مِّنَ الْكُفَّارِ وَلْيَجِدُوا فِيكُمْ غِلْظَةً ۚ وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ مَعَ الْمُتَّقِينَ (123) وَإِذَا مَا أُنزِلَتْ سُورَةٌ فَمِنْهُم مَّن يَقُولُ أَيُّكُمْ زَادَتْهُ هَٰذِهِ إِيمَانًا ۚ فَأَمَّا الَّذِينَ آمَنُوا فَزَادَتْهُمْ إِيمَانًا وَهُمْ يَسْتَبْشِرُونَ (124) وَأَمَّا الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ فَزَادَتْهُمْ رِجْسًا إِلَىٰ رِجْسِهِمْ وَمَاتُوا وَهُمْ كَافِرُونَ (125) أَوَلَا يَرَوْنَ أَنَّهُمْ يُفْتَنُونَ فِي كُلِّ عَامٍ مَّرَّةً أَوْ مَرَّتَيْنِ ثُمَّ لَا يَتُوبُونَ وَلَا هُمْ يَذَّكَّرُونَ (126) وَإِذَا مَا أُنزِلَتْ سُورَةٌ نَّظَرَ بَعْضُهُمْ إِلَىٰ بَعْضٍ هَلْ يَرَاكُم مِّنْ أَحَدٍ ثُمَّ انصَرَفُوا ۚ صَرَفَ اللَّهُ قُلُوبَهُم بِأَنَّهُمْ قَوْمٌ لَّا يَفْقَهُونَ (127) لَقَدْ جَاءَكُمْ رَسُولٌ مِّنْ أَنفُسِكُمْ عَزِيزٌ عَلَيْهِ مَا عَنِتُّمْ حَرِيصٌ عَلَيْكُم بِالْمُؤْمِنِينَ رَءُوفٌ رَّحِيمٌ (128) فَإِن تَوَلَّوْا فَقُلْ حَسْبِيَ اللَّهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ۖ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ ۖ وَهُوَ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ (129)
الصفحة Page 207
(123) Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yãƙi waɗanda suke kusantar ku daga kãfirai. Kuma su sami tsanani daga gare ku. Kuma ku sani cẽwa Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa.
(124) Kuma idan aka saukar da wata sũra, to, daga gare su akwai waɗanda suke cẽwa: "Wãne a cikinku wannan sũra ta ƙãra masa ĩmãni?" To amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sũ, sunã yin bushãra (da ita).
(125) Amma kuma waɗanda suke a cikin zukãtansu akwai cũta, to, tã ƙãra musu ƙazanta zuwa ga ƙazantarsu, kuma su mutu alhãlin kuwa sunã kãfirai.
(126) Shin, bã su ganin cẽwa anã fitinar su a cikin kõwace shẽkara: Sau ɗaya kõ kuwa sau biyu, sa'an nan kuma bã su tũba, kuma ba su zama sunã tunãni ba?
(127) "Kuma idan haƙĩƙa, aka saukar da wata sũra, sai sãshensu ya yi dũbi zuwa ga wani sãshe, (su ce): "Shin, wani mutum yanã ganin ku?" Sa'an nan kuma sai su jũya. Allah Ya jũyar da zukãtansu, dõmin, haƙĩƙa sũ mutãne ne, bã su fahimta.
(128) Lalle ne, haƙĩƙa, Manzo daga cikinku yã je muku. Abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa. Mai kwaɗayi ne sabõda ku. Ga muminai Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.
(129) To, idan sun jũya, sai ka ce: Ma'ishĩna Allah ne. Bãbu abin bautãwa fãce shi. A gare Shi nake dõgara. Kuma Shi ne Ubangijin Al'arshi mai girma.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022