(68) Kuma aka busa a cikin ƙaho, sai waɗanda ke a cikin sammai da ƙasã suka sũma sai wanda Allah Ya so (rashin sumansa) sa'an nan aka hũra a cikinsa, wata hũrãwa, sai gã su tsaitsaye, sunã kallo.
(69) Kuma ƙasã ta yi haske da hasken Ubangijinta, kuma aka aza littãfi, kuma aka zo da Annabãwa da mãsu shaida, kuma aka yi hukunci a tsakãninsu, da gaskiya, alhãli kuwa, sũ, bã zã a zãlunce su ba.
(70) Kuma aka cika wa kõwane rai abin da ya aikata. Kuma (Allah) Shĩ ne Mafi sani game da abin da suke aikatãwa.
(71) Kuma aka kõra waɗanda suka kãfirta zuwa Jahannama, jama'a-jama'a har a lõkacin da suka je mata, sai aka buɗe ƙõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, "Ashe, waɗansu Manzanni, daga cikinku ba su je muku ba, sunã karanta ãyõyin Ubangijinku a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin gamuwa da yininku wannan?" Suka ce, "Na'am, "kuma amma kalmar azãba ita ce ta wajaba a kan kãfirai!"
(72) Aka ce, "Ku shiga ƙõfõfin Jahannama, kaunã madawwama a cikinta. Sa'an nan mazaunin makangara yã munana."
(73) Kuma aka kõra waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa zuwa Aljanna jama'a-jama'a har a lõkacin da suka jẽ mata, alhãli kuwa an buɗe kõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, "Aminci ya tabbata a gare ku, kun ji dãɗi, sabõda haka ku shige ta, kunã madawwama (a cikinta)."
(74) Kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya yi mana gaskiya ga wa'adinSa, kuma Ya gãdar da mu ƙasã, munã zama a cikin Aljanna a inda muke so." To, madalla da ijãrar ma'aikata.