(62) Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka tũba, da Nasãra da Makarkata, wana ya yi ĩmani da Allah da Yinin Lãhira, kuma ya aikata aikin ƙwarai, to, suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba.
(63) Kuma a lõkacin da Muka riƙi alƙawarinku, kuma Muka ɗaukaka dũtse a bisa gareku: "Ku kãma abin da Muka baku da ƙarfi. Kuma ku ambaci abin da yake a cikin sa, tsammãninku ku kãrekanku.
(64) Sa'an nan kuma kuka jũya daga bayan wancan, to, bã dõmin falalar Allah ba da rahamarSa a kanku, haƙĩƙa, dã kun kasance daga mãsu hasãra."
(65) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, kun san waɗanda suka ƙẽtare haddi daga gare ku a cikin Asabar, sai muka ce musu: "ku kasance birai ƙasƙantattu."
(66) Muka sanya ta (mas'alar) azãba, dõmin abin da yake gaba gareta, da yake a bãyanta, kuma wa'azi ga mãsu taƙawa.
(67) Kuma a lõkacin da Musa yace ga mutanensa: "Lalle ne, Allah Yana umurtar ku da ku yanka wata sãniya." Suka ce: "Shin kana riƙon mu ne da izgili?" Ya ce: "Ina nẽman tsari daga Allah da in kasance daga jãhilai."
(68) Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana, mecẽ ce ita?" Ya ce: "Lalle ne, Shi, Yana cewa: "Lalle ne ita sãniya ce; bã tsõfuwa ba, bã kuma budurwa ba, tsakãtsaki ce a tsakãnin wancan,' sai ku aikata abin da ake umurninku."
(69) Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka Ya bayyana mana abin da yake launinta." Ya ce: "Lalle ne, Shi Yana cewa: "Ita wata saniya ce fatsa-fatsa, mai tsan-tsan launi, tana faranta ran mausu kallonta."