(38) Kuma Yanã sassaƙa jirgin cikin natsuwa, kuma a kõ yaushe waɗansu shugabanni daga mutãnensa suka shũɗe a gabansa, sai su yi izgili gare shi. Ya ce: "Idan kun yi izgili gare mu, to, haƙĩƙa mũ mã zã mu yi izgili gare ku, kamar yadda kuke yin izgili.
(39) "Sa'an nan da sannu zã ku san wanda azãba zã ta zo masa, ta wulakantã shi (a dũniya), kuma wata azãba zaunanna ta sauka a kansa (a Lãhira)."
(40) Har a lõkacin da umurninMu ya je, kuma tandã ta ɓulɓula. Muka ce: "Ka ɗauka, a cikinta, daga kõme, ma'aura biyu, da kuma iyalanka, fãce wanda magana ta gabãta a kansa, da wanda ya yi ĩmãni." Amma kuma bãbu waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi fãce kaɗan."
(41) Kuma ya ce: "Ku hau a cikinta, da sũnan Allah magudãnarta da matabbatarta. Lalle ne Ubangijĩna, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
(42) Kuma ita tanã gudãna da su a cikin tãguwar ruwa kamai duwãtsu, sai Nũhu ya kirãyi ɗansa alhãli, kuwa ya kasance can wuri mai nĩsa. "Yã ƙaramin ɗãnã! zo ka hau tãre da mu, kuma kada ka kasance tãre da kãfirai!"
(43) Ya ce: "Zan tattara zuwa ga wani dũtse ya tsare ni daga ruwan." (Nũhu) ya ce: "Bãbu mai tsarẽwa a yau daga umurnin Allah fãce wanda Ya yi wa rahama." Sai taguwar ruwa ta shãmakace a tsakãninsu, sai ya kasance daga waɗanda aka nutsar.
(44) Kuma aka ce: "Yã ƙasa! Ki haɗiye ruwanki, kuma yã sama! Ki kãme."Kuma aka faƙar da ruwan kuma aka hukunta al'amarin, kuma Jirgin ya daidaita a kan Jũdiyyi, kuma aka ce: "Nĩsa ya tabbata ga mutãne azzãlumai."
(45) Kuma Nũhu ya kira Ubangijinsa, sa'an nan ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne ɗãna na daga iyãlĩna! Kuma haƙĩƙa wa'adinKa gaskiya ne, kuma Kai ne Mafi hukuncin mãsu yin hukunci."