البقرة   سورة  : Al-Baqara


سورة Sura   البقرة   Al-Baqara
قُلْنَا اهْبِطُوا مِنْهَا جَمِيعًا ۖ فَإِمَّا يَأْتِيَنَّكُم مِّنِّي هُدًى فَمَن تَبِعَ هُدَايَ فَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ (38) وَالَّذِينَ كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ (39) يَا بَنِي إِسْرَائِيلَ اذْكُرُوا نِعْمَتِيَ الَّتِي أَنْعَمْتُ عَلَيْكُمْ وَأَوْفُوا بِعَهْدِي أُوفِ بِعَهْدِكُمْ وَإِيَّايَ فَارْهَبُونِ (40) وَآمِنُوا بِمَا أَنزَلْتُ مُصَدِّقًا لِّمَا مَعَكُمْ وَلَا تَكُونُوا أَوَّلَ كَافِرٍ بِهِ ۖ وَلَا تَشْتَرُوا بِآيَاتِي ثَمَنًا قَلِيلًا وَإِيَّايَ فَاتَّقُونِ (41) وَلَا تَلْبِسُوا الْحَقَّ بِالْبَاطِلِ وَتَكْتُمُوا الْحَقَّ وَأَنتُمْ تَعْلَمُونَ (42) وَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ وَارْكَعُوا مَعَ الرَّاكِعِينَ (43) ۞ أَتَأْمُرُونَ النَّاسَ بِالْبِرِّ وَتَنسَوْنَ أَنفُسَكُمْ وَأَنتُمْ تَتْلُونَ الْكِتَابَ ۚ أَفَلَا تَعْقِلُونَ (44) وَاسْتَعِينُوا بِالصَّبْرِ وَالصَّلَاةِ ۚ وَإِنَّهَا لَكَبِيرَةٌ إِلَّا عَلَى الْخَاشِعِينَ (45) الَّذِينَ يَظُنُّونَ أَنَّهُم مُّلَاقُو رَبِّهِمْ وَأَنَّهُمْ إِلَيْهِ رَاجِعُونَ (46) يَا بَنِي إِسْرَائِيلَ اذْكُرُوا نِعْمَتِيَ الَّتِي أَنْعَمْتُ عَلَيْكُمْ وَأَنِّي فَضَّلْتُكُمْ عَلَى الْعَالَمِينَ (47) وَاتَّقُوا يَوْمًا لَّا تَجْزِي نَفْسٌ عَن نَّفْسٍ شَيْئًا وَلَا يُقْبَلُ مِنْهَا شَفَاعَةٌ وَلَا يُؤْخَذُ مِنْهَا عَدْلٌ وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ (48)
الصفحة Page 7
(38) Muka ce: "Ku ku sauka daga gare ta gabã ɗaya. To, imma lalle shiriya ta je muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiriya ta to, bãbu tsõro a kansu, kuma bã su yin baƙin ciki."
(39) "Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗannan sũ ne abõkan Wuta; sũ a cikinta madawwama ne."
(40) Yã Banĩ Isrã'Ĩla! Ku tuna ni'imãTa a kanku, kuma ku cika alƙawariNa, In cika muku da alƙawarinku. kuma Ni, ku ji tsõro Na.
(41) Kuma, ku yi ĩmãni da abin da na saukar, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku, kuma kada ku kasance farkon kãfiri game da shi, Kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ãyõyiNa. Kuma ku ji tsõrõNa, Nĩ kaɗai.
(42) Kuma kada ku lulluɓe gaskiya da ƙarya, kuma ku ɓõye gaskiya, alhãli kuwa kuna sane.
(43) Kuma ku tsayar da salla; kuma ku bãyar da zakka; kuma ku yi rukũ'i tãre da mãsu yin rukũ'i.
(44) Shin, kuna umurnin mutãne da alhẽri, kuma ku manta da kanku alhãli kuwa kuna karatun littãfi? Shin, bãzã ku hankalta ba?
(45) Kuma ku nẽmi taimako da yin haƙuri, da salla. Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa, mai girma ce fãce fa a kan mãsu tsõron Allah.
(46) Waɗanda suka tabbata cẽwa lalle ne su mãsu haɗuwa da Ubangijinsu, kuma lalle ne sũ a gareshi mãsu kõmãwa ne.
(47) Yã banĩ Isrã'ĩla! Ku tuna ni'imaTa, wadda Na ni'imta a kanku, kuma lalle ne Ni, na fĩfĩta ku a kan tãlikai.
(48) Kuma ku ji tsron wani yini, (a cikinsa) rai bã ya Wadãtar da wani rai da kõme, kuma bã a karɓar cetõ daga gareshi, kuma ba a karɓar fansa daga gare shi, kuma bã su zama ana taimakon su ba.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022