الأحقاف   سورة  : Al-Ahqaf


سورة Sura   الأحقاف   Al-Ahqaf
۞ وَاذْكُرْ أَخَا عَادٍ إِذْ أَنذَرَ قَوْمَهُ بِالْأَحْقَافِ وَقَدْ خَلَتِ النُّذُرُ مِن بَيْنِ يَدَيْهِ وَمِنْ خَلْفِهِ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا اللَّهَ إِنِّي أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ (21) قَالُوا أَجِئْتَنَا لِتَأْفِكَنَا عَنْ آلِهَتِنَا فَأْتِنَا بِمَا تَعِدُنَا إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ (22) قَالَ إِنَّمَا الْعِلْمُ عِندَ اللَّهِ وَأُبَلِّغُكُم مَّا أُرْسِلْتُ بِهِ وَلَٰكِنِّي أَرَاكُمْ قَوْمًا تَجْهَلُونَ (23) فَلَمَّا رَأَوْهُ عَارِضًا مُّسْتَقْبِلَ أَوْدِيَتِهِمْ قَالُوا هَٰذَا عَارِضٌ مُّمْطِرُنَا ۚ بَلْ هُوَ مَا اسْتَعْجَلْتُم بِهِ ۖ رِيحٌ فِيهَا عَذَابٌ أَلِيمٌ (24) تُدَمِّرُ كُلَّ شَيْءٍ بِأَمْرِ رَبِّهَا فَأَصْبَحُوا لَا يُرَىٰ إِلَّا مَسَاكِنُهُمْ ۚ كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْقَوْمَ الْمُجْرِمِينَ (25) وَلَقَدْ مَكَّنَّاهُمْ فِيمَا إِن مَّكَّنَّاكُمْ فِيهِ وَجَعَلْنَا لَهُمْ سَمْعًا وَأَبْصَارًا وَأَفْئِدَةً فَمَا أَغْنَىٰ عَنْهُمْ سَمْعُهُمْ وَلَا أَبْصَارُهُمْ وَلَا أَفْئِدَتُهُم مِّن شَيْءٍ إِذْ كَانُوا يَجْحَدُونَ بِآيَاتِ اللَّهِ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُوا بِهِ يَسْتَهْزِئُونَ (26) وَلَقَدْ أَهْلَكْنَا مَا حَوْلَكُم مِّنَ الْقُرَىٰ وَصَرَّفْنَا الْآيَاتِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ (27) فَلَوْلَا نَصَرَهُمُ الَّذِينَ اتَّخَذُوا مِن دُونِ اللَّهِ قُرْبَانًا آلِهَةً ۖ بَلْ ضَلُّوا عَنْهُمْ ۚ وَذَٰلِكَ إِفْكُهُمْ وَمَا كَانُوا يَفْتَرُونَ (28)
الصفحة Page 505
(21) Kuma ka ambaci ɗan'uwan Ãdãwa a lõkacin da ya yi gargaɗi ga mutãnensa, a Tuddan Rairayi, alhãli kuwa waɗansu mãsu gargaɗi sun shũɗe agaba gare shi da bãya gare shi (da cẽwa) "Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah. Lalle nĩ inã tsõrata muku azãbar yini mai girma."
(22) Suka ce: "Shin, kã zo mana ne dõmin ka karkatar da mu daga gumãkaumu? To, ka zo mana da abin da kake yi mana wa'adin, idan kã kasance daga mãsu gaskiya."
(23) Ya ce: "Ilimi a wurin Allah kawai yake, kuma inã iyar maku abin da aka aiko ni da shi, kuma amma inã ganin, kũ, wasu mutãne ne, kunã jãhiltar gaskiya."
(24) To, a lõkacin da suka ga azãbar, kumar hadari mai fuskantar rãfukansu, suka ce: "Wannan hadari ne mai yi mana ruwa. Ã'a, shĩ na abin da kuke nẽman gaggawar saukarsa; Iska ce, a cikinta akwai wata azaba mai raɗaɗi.
(25) Tanã darkake kõwane abu da umurnin Ubangijinta. Sai suka wãyi gari, bã a ganin kõme fãce gidãjensu. Kamar wannan ne Muke sãka wa mutãne mãsu laifi.
(26) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun ba su ĩko ga abin da ba Mubã ku ĩko gare shi ba, kuma Muka sanya musu wani irin jĩ da gani dazukãta. Sai dai jnsu bai amfãne su ba, kuma zukãtansu ba su amfãne su ba ga kõme, dõmin sun kasance sunã musu game da ãyõyin Allah, kuma abin da suka kasance sunã aikatãwa na izgili game da shi ya wajaba a gare su.
(27) Kuma ne, lalle haƙĩƙa, Mun halakar da abin da yake kẽwayenku na alƙaryu kuma Muka jujjũya ãyõyi, tsammãninsu zã su kõmo.
(28) To, don mẽne ne waɗanda suka riƙa, baicin Allah, abũbuwan yi. wa baiko, gumaka, ba su taimake su ba? Ã'a, sun ɓace musu Kuma wannan shi ne ƙiren ƙaryarsu da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022