(45) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, mun aika zuwa Samũdãwa da ɗan'uwansu, Salihu (ya ce), "Ku bauta wa Allah." Sai gã su ƙungiyõyi biyu sunã ta husũma.
(46) Ya ce: "Yã mutãnẽna! Don me kuke nẽman gaggãwa game da mũnanãwa, a gabãnin kyautatãwa. Don me bã ku nẽman Allah gãfara, tsammãninku, zã a yi muku rahama?"
(47) Suka ce: "Munã shu'umci da kai, kuma da wanda ke tãre da kai." Ya ce: "Shu'umcinku a wurin Allah yake. Ã'a, kũ mutãne ne, anã fitinar ku."
(48) Kuma waɗansu jama'a tara sun kasance a cikin birnin, sunã yin ɓarna, kuma bã su kyautatãwa. Suka ce: "Ku yi rantsuwa da Allah, lalle zã mu kwãnan masa, shi da mutãnensa sa'an nan mu ce wa waliyyinsa. 'Ba mu halarci halakar mutãnensa ba kuma mũ, haƙĩ ƙa, mãsu gaskiya ne'."
(49) Kuma suka ƙulla mãkirci, kuma Muka ƙulla sakamakon mãkirci, alhãli sũ ba su sani ba.
(50) Ka dũba yadda ãƙibar mãkircinsu ta kasance lalle Mũ Mun darkãke su da mutãnensu, gabã ɗaya.
(51) Waɗancan, gidãjensu ne, wõfintattu sabõda zãluncin da suka yi, lalle ne a wancan akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke sani.
(52) Muka tsĩrar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sun kasance sunã taƙawa.
(53) Da Lũdu, a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, "Shin kunã jẽ wa alfasha ne, alhãli, kuwa kunã gani?"
(54) "Shin lalle kũ haƙĩƙa kunã je wa maza da sha'awa baicin mãtã? Ã'a, kũ wasu irin mutãne ne kuna aikin jãhilci."
(55) 49.