النبإ   سورة  : An-Naba


سورة Sura   النبإ   An-Naba
النبإ An-Naba
عَمَّ يَتَسَاءَلُونَ (1) عَنِ النَّبَإِ الْعَظِيمِ (2) الَّذِي هُمْ فِيهِ مُخْتَلِفُونَ (3) كَلَّا سَيَعْلَمُونَ (4) ثُمَّ كَلَّا سَيَعْلَمُونَ (5) أَلَمْ نَجْعَلِ الْأَرْضَ مِهَادًا (6) وَالْجِبَالَ أَوْتَادًا (7) وَخَلَقْنَاكُمْ أَزْوَاجًا (8) وَجَعَلْنَا نَوْمَكُمْ سُبَاتًا (9) وَجَعَلْنَا اللَّيْلَ لِبَاسًا (10) وَجَعَلْنَا النَّهَارَ مَعَاشًا (11) وَبَنَيْنَا فَوْقَكُمْ سَبْعًا شِدَادًا (12) وَجَعَلْنَا سِرَاجًا وَهَّاجًا (13) وَأَنزَلْنَا مِنَ الْمُعْصِرَاتِ مَاءً ثَجَّاجًا (14) لِّنُخْرِجَ بِهِ حَبًّا وَنَبَاتًا (15) وَجَنَّاتٍ أَلْفَافًا (16) إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ كَانَ مِيقَاتًا (17) يَوْمَ يُنفَخُ فِي الصُّورِ فَتَأْتُونَ أَفْوَاجًا (18) وَفُتِحَتِ السَّمَاءُ فَكَانَتْ أَبْوَابًا (19) وَسُيِّرَتِ الْجِبَالُ فَكَانَتْ سَرَابًا (20) إِنَّ جَهَنَّمَ كَانَتْ مِرْصَادًا (21) لِّلطَّاغِينَ مَآبًا (22) لَّابِثِينَ فِيهَا أَحْقَابًا (23) لَّا يَذُوقُونَ فِيهَا بَرْدًا وَلَا شَرَابًا (24) إِلَّا حَمِيمًا وَغَسَّاقًا (25) جَزَاءً وِفَاقًا (26) إِنَّهُمْ كَانُوا لَا يَرْجُونَ حِسَابًا (27) وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا كِذَّابًا (28) وَكُلَّ شَيْءٍ أَحْصَيْنَاهُ كِتَابًا (29) فَذُوقُوا فَلَن نَّزِيدَكُمْ إِلَّا عَذَابًا (30)
الصفحة Page 582
النبإ An-Naba
(1) A kan mẽ suke tambayar jũna?
(2) A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)?
(3) Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa?
(4) A'aha! Zã su sani.
(5) Kuma, a'aha! Zã su sani.
(6) Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba?
(7) Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)?
(8) Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã?
(9) Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa?
(10) Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?
(11) Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci?
(12) Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi?
(13) Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)?
(14) Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba?
(15) Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi?
(16) Da itãcen lambuna mãsu lillibniya?
(17) Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci.
(18) Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a.
(19) Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi.
(20) Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra.
(21) Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata.
(22) Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma.
(23) Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna.
(24) Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha.
(25) Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini.
(26) Sakamako mai dãcẽwa.
(27) Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi.
(28) Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyinMu, ƙaryatãwa!
(29) Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce.
(30) Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022