(31) (Ibrãĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni!"
(32) Suka ce: "Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi.
(33) "Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu (bom).
(34) "Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna."
(35) Sa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai.
(36) Sai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi.
(37) Kuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi.
(38) Kuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne.
(39) Sai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci!"
(40) Sabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
(41) Kuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙẽƙasasshiya a kansu.
(42) Bã ta barin kõme da ta jẽ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasũsuwa.
(43) Kuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: "Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci,"
(44) Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsãwa ta kãma su, alhãli kuwa sunã kallo.
(45) Ba su kõ sãmu dãmar tsayãwa ba, kuma ba su kasance mãsu nẽman ãgaji ba.
(46) Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.
(47) Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhãli kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatãwa.
(48) Kuma ƙasã Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ,
(49) Kuma daga kõme Mun halitta nau'i biyu, watakila zã ku yi tunãni.
(50) Sabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.
(51) Kuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.