(9) Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan anyi kirã zuwã ga salla a rãnar Jumu'a, sai ku yi aiki zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar ciniki. Wancan ɗinku ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani.
(10) Sa'an nan idan an ƙarẽ salla, Sai ku wãtsu a cikin ƙasã kuma ku nẽma daga falalar Allah, kuma ku ambaci sũnan Allah da yawa ɗammãninku, ku sãmi babban rabo.
(11) Kuma idan suka ga wani fatauci kõ kuma wani wasan shagala, sai su yi rũgũguwar fita zuwa gare su, kuma su bar ka kanã tsaye. Ka ce: "Abin da yake a wurin Allah ne mafi alhẽri daga fataucin, alhãli kuwa Allah ne Mafi alhẽrinmãsu arzũtãwa."
المنافقون Al-Munaafiqoon
(1) Idan munãfukai suka jẽ maka suka ce: "Munẽ shaidar lalle kai haƙĩƙa Manzon Allah ne," Kuma Allah Yanã sane da lalle Kai, haƙĩƙa ManzonSa ne, kuma Allah Yanã shaida lalle munafukan haƙĩƙa, maƙaryata ne.
(2) Sun riƙi rantsuwõwinsu garkuwa, sai suka taushe daga tafarkin Allah. Lalle sũ abin da suka kasance sunã aikatãwa ya mũnana.
(3) Wancan, dõmin lalle sũ, sun yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka kãfirta, sai aka yunƙe a kan zukãtansu. Sabõda sũ, bã su fahimta.
(4) Kuma idan kã gan su, sai jikunansu su bã ka sha'awa kuma idan sun faɗa, zã ka saurãra ga maganarsu. Kamar dai sũ ƙyami ne wanda aka jingine. Sunã zaton kõwace tsãwa a kansu take. Sũ ne maƙiyan, sai ka yi saunarsu. Allah Yã la'ane su. Yãya ake karkatar da su?