(52) Kuma Muka kira shi daga gẽfen dũtse na dãma kuma Muka kusanta shi yanã abõkin gãnãwa.
(53) Kuma Muka yi masa kyauta daga RahamarMu da ɗan'uwansa Hãrũna, ya zama Annabi.
(54) Kuma ka ambaci Ismã'ila a cikin Littãfi. Lalle shi, yã kasance mai gaskiyar alkawari, kuma yã kasance Manzo, Annabi.
(55) Kuma yã kasance yanã umurnin mutãnens da salla da zakka. Kuma yã kasance yardajje a wurin Ubangijinsa.
(56) Kuma ka ambaci Idrĩsa a cikin Littãfi. Lalle shi, ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi.
(57) Muka ɗaukaka shi a wuri maɗaukaki.
(58) Waɗancan sũ ne waɗanda Allah Ya yi wa ni'ima daga Annabãwa daga zurriyar Ãdamu, kuma daga waɗanda muka ɗauka tãre da Nũhu, kuma daga zurriyar Ibrãhĩm da Isrã'ila, kuma daga waɗanda Muka shiryar kuma Muka zãɓe su. Idan anã karãtun ãyõyin Mai rahama a kansu, sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma mãsu kũka.
(59) Sai waɗansu 'yan bãya suka maye a bãyansu suka tõzarta salla, kuma suka bi sha'awõwinsu. To, da sannu zã su hau da wani sharri.
(60) Fãce wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai. To, waɗannan sunã shiga Aljanna, kuma bã a zãluntar su da kõme.
(61) Gidãjen Aljannar zama wadda Mai rahama ya yi alkawarin bãyarwa ga bãyinSa (mãsu aikin ĩmãni) a fake. Lalle ne shĩ, alkawarin ya kasance abin riskuwa.
(62) Bã su jin yasassar magana a cikinta, fãce sallama. Kuma sunã da abinci, a cikinta, sãfe da maraice.
(63) Wancan Aljannar ce wadda Muke gãdar da wanda ya kasance mai aiki da taƙawa daga bãyiNa.
(64) (Sunã mãsu cẽwa) "Kuma bã mu sauka Fãce da umuruin Ubangijinka (Muhammad). Shĩ ne da mulkin abin da ke a gaba gare mu da abin da ke a bãyanmu da abin da ke a tsakãnin wannan." Kuma (Ubangijinka bai kasance wanda ake mantãwa ba.