(20) Ya ce: "Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin hushi."
(21) "Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni."
(22) "Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla."
(23) Fir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu?"
(24) Ya ce: "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu ƙarfin ĩmãni."
(25) Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, "Bã za ku saurãra ba?"
(26) Ya ce: "Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko."
(27) Ya ce: "Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne."
(28) Ya ce: "Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kunã hankalta."
(29) Ya ce: "Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga ɗaurarru."
(30) Ya ce: "Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa?"
(31) Ya ce: "To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya."
(32) Sai ya jẽfa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne.
(33) Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo.
(34) (Fir'auna) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, "Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci ne, mai ilmi!
(35) "Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke shãwartãwa?"
(36) Suka ce: "Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a cikin birãne."
(37) "Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani."
(38) Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne.
(39) Kuma aka ce wa mutãne "Kõ kũ mãsu tãruwã ne?