الشورى   سورة  : Ash-Shura


سورة Sura   الشورى   Ash-Shura
وَمِنْ آيَاتِهِ الْجَوَارِ فِي الْبَحْرِ كَالْأَعْلَامِ (32) إِن يَشَأْ يُسْكِنِ الرِّيحَ فَيَظْلَلْنَ رَوَاكِدَ عَلَىٰ ظَهْرِهِ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّكُلِّ صَبَّارٍ شَكُورٍ (33) أَوْ يُوبِقْهُنَّ بِمَا كَسَبُوا وَيَعْفُ عَن كَثِيرٍ (34) وَيَعْلَمَ الَّذِينَ يُجَادِلُونَ فِي آيَاتِنَا مَا لَهُم مِّن مَّحِيصٍ (35) فَمَا أُوتِيتُم مِّن شَيْءٍ فَمَتَاعُ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۖ وَمَا عِندَ اللَّهِ خَيْرٌ وَأَبْقَىٰ لِلَّذِينَ آمَنُوا وَعَلَىٰ رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ (36) وَالَّذِينَ يَجْتَنِبُونَ كَبَائِرَ الْإِثْمِ وَالْفَوَاحِشَ وَإِذَا مَا غَضِبُوا هُمْ يَغْفِرُونَ (37) وَالَّذِينَ اسْتَجَابُوا لِرَبِّهِمْ وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ وَأَمْرُهُمْ شُورَىٰ بَيْنَهُمْ وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنفِقُونَ (38) وَالَّذِينَ إِذَا أَصَابَهُمُ الْبَغْيُ هُمْ يَنتَصِرُونَ (39) وَجَزَاءُ سَيِّئَةٍ سَيِّئَةٌ مِّثْلُهَا ۖ فَمَنْ عَفَا وَأَصْلَحَ فَأَجْرُهُ عَلَى اللَّهِ ۚ إِنَّهُ لَا يُحِبُّ الظَّالِمِينَ (40) وَلَمَنِ انتَصَرَ بَعْدَ ظُلْمِهِ فَأُولَٰئِكَ مَا عَلَيْهِم مِّن سَبِيلٍ (41) إِنَّمَا السَّبِيلُ عَلَى الَّذِينَ يَظْلِمُونَ النَّاسَ وَيَبْغُونَ فِي الْأَرْضِ بِغَيْرِ الْحَقِّ ۚ أُولَٰئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ (42) وَلَمَن صَبَرَ وَغَفَرَ إِنَّ ذَٰلِكَ لَمِنْ عَزْمِ الْأُمُورِ (43) وَمَن يُضْلِلِ اللَّهُ فَمَا لَهُ مِن وَلِيٍّ مِّن بَعْدِهِ ۗ وَتَرَى الظَّالِمِينَ لَمَّا رَأَوُا الْعَذَابَ يَقُولُونَ هَلْ إِلَىٰ مَرَدٍّ مِّن سَبِيلٍ (44)
الصفحة Page 487
(32) Kuma akwai daga ãyõyinsa, jirãge mãsu gudãna a cikin tẽku kamar duwãtsu.
(33) Idan Ya so, sai Ya kwantar da iskar, sai jirãgen su yini sunã mãsu kawaici a kan bãyan tẽkun, Lalle ne ga wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga dukan mai haƙuri, Mai gõdiya.
(34) Kõ Ya halakã su (sũ jirãgen) sabõda abin da mãsu su suka sanã'anta, alhãli kuwa Yanã yãfe (laifuffuka) mãsu yawa.
(35) Kuma dõmin waɗanda ke jãyayya a cikin ãyõyinMu su sani (cẽwa) bã su da wata mafaka.
(36) Sabõda haka abin da aka bã ku, kõ mẽne ne, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne, kuma abin da ke a wurin Allah Shĩ ne mafĩfĩci, kuma Shĩ ne mafi wanzuwa ga waɗanda suka yi ĩmãni kuma sunã dõgara a kan Ubangijinsu kawai.
(37) Kuma waɗanda ke nisantar manyan zunubbai da ayyukan alfãsha, kuma idan sun yi fushi, sũ, sunã gãfartawa.
(38) Da waɗanda suka karɓa kira ga Ubangijinsu, kuma suka tsayar da salla, kuma al'amarinsu shãwara ne a tsakãninsu, kuma daga abin da Muka azurta su sunã ciyarwa.
(39) Da waɗanda idan zãlunci ya sãme su, sunã nẽman taimako (su rãma).
(40) Kuma sakamakon cũta shĩ ne wata cũta kamarta, sai dai wanda Ya yãfe kuma ya kyautata, to lãdarsa nã ga Allah. Lalle ne, Shĩ (Allah) bã Ya son azzãlumai.
(41) Kuma Lalle ne, wanda ya nẽmi taimakon rãmãwa a bãyan an zãlunce shi, to waɗannan bãbu wata hanyar zargi a kansu.
(42) lnda hanyar zargi kawai take, shĩ ne a kan waɗanda ke zãluntar mutãne kuma sunã ƙẽtare haddin shari'a cikin ƙasa bã tare da haƙƙi ba. Waɗannan sunã da azãba Mai raɗaɗi.
(43) Kuma Lalle ne, wanda ya yi haƙuri kuma ya gãfarta (wa wanda ya zãlunce shi), to shĩ wancan aiki haƙĩƙa, yanã daga manyan al'amura (da Allah ke so).
(44) Kuma wanda (Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani majiɓinci bãyanSa, kuma zã ka ga azzãlumai, a lõkacin da suka ga azãba, sunã cẽwa, "Shin, akwai hanya zuwa ga kõmãwa?"
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022