(36) Kuma ba ya halatta ga mũmini kuma haka ga mũmina, a lõkacin da Allah da Manzonsa Ya hukunta wani umurni, wani zãɓi daga al'amarinsu ya kasance a gare su. Kuma wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa, to, yã ɓace, ɓacẽwa bayyananna.
(37) Kuma a lõkacin da kake cẽwa ga wanda Allah Ya yi ni'ima a gare shi kai kuma ka yi ni'ima a gare shi, "Ka riƙe mãtarka, kuma ka bi Allah da taƙawa," kuma kana ɓõyẽwa a cikin ranka abin da Allah zai bayyana shi, kanã tsõron mutãne, alhãli kuwa Allah ne Mafi cancantar ka ji tsõronSa. to a lõkacin da zaidu ya ƙãre bukãtarsa daga gare ta, Mun aurar da kai ita, dõmin kada wani ƙunci ya kasance a kan mũminai a cikin (auren mãtan) ɗiyan hankãkarsu, idan sun ƙãre bukãta daga gare su. Kuma umurnin Allah yã kasance abin aikatãwa.
(38) Wani ƙunci bai kasance a kan Annabi ba ga abin da Allah Ya faralta a kansa, a kan ƙã'idar, Allah a cikin (Annabãwa) waɗanda suka shige daga gabãninsa. Kuma umurnin Allah yã kasance abin ƙaddarãwa tabbatacce.
(39) Waɗanda ke iyar da Manzancin Allah, kuma sunã tsõronSa, kuma bã su tsõron kõwa fãce Allah, Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai hisabi.
(40) Muhammadu bai kasance uban kõwa ba daga mazanku, kuma amma shĩ yã kasance Manzon Allah kuma cikon Annabãwa. Kuma Allah Ya kasance Masani ga kõme.
(41) Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ambaci Allah, ambata mai yawa.
(42) Kuma ku tsarkake shi, a sãfiya da maraice.
(43) (Allah) Shĩ ne Wanda ke tsarkake ku, da mala'ikunSa (sunã yi muku addu'a), dõmin Ya fitar da ku daga duffai zuwa ga haske. Kuma (Allah) Yã kasance Mai Jĩn ƙai ga mũminai.