(118) Kuma (Allah) Yã karɓi tũba a kan ukun nan waɗanda aka jinkirtar har ƙasa da yalwarta ta yi ƙunci a kansu, kuma rãyukansu suka yi ƙunci a kansu, kuma suka yi zaton bãbu wata mafakã daga Allah fãce (kõmãwa) zuwa gare Shi. Sa'an nan Allah Ya karɓi tũbarsu, dõmin su tabbata a kan tũba. Lalle Allah ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.
(119) Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, kuma ku kasance tãre da mãsu gaskiya.
(120) Bã ya kasancẽwa ga mutãnen Madĩna da wanda yake a gẽfensu, daga ƙauyãwã, su sãba daga bin Manzon Allah, kuma kada su yi gudu da rãyukansu daga ransa. Wancan, sabõda ƙishirwa bã ta sãmun su, haka kuma wata wahala, haka kuma wata yunwa, a cikin hanyai Allah, kuma bã su tãkin wani matãki wanda yake takaitar da kãfirai kuma bã su sãmun wani sãmu daga maƙiyi fãce an rubuta musu da shi, lãdar aiki na ƙwarai. Lallai ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa.
(121) Kuma bã su ciyar da wata ciyarwa, ƙarama kõ babba, kuma bã su kẽta wani rafi sai an rubutã musu, dõmin Allah Ya sãka musu da mafi kyãwon abin da suka kasance sunã aikatãwa.
(122) Kuma bã ya kasancẽwã ga muminai su fita zuwa yãƙi gabã ɗaya. Sabõda haka, don me ne wata jama'a daga kowane ɓangare daga gare su ba ta fita (zuwa nẽman ilimi ba) dõmin su nẽmi ilimi ga fahimtar addĩni kuma dõmin su yi gargaɗi ga mutãnensu idan sun kõma zuwa gare su, tsammãninsu, sunã yin sauna?