المؤمنون   سورة  : Al-Muminoon


سورة Sura   المؤمنون   Al-Muminoon
أَلَمْ تَكُنْ آيَاتِي تُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ فَكُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ (105) قَالُوا رَبَّنَا غَلَبَتْ عَلَيْنَا شِقْوَتُنَا وَكُنَّا قَوْمًا ضَالِّينَ (106) رَبَّنَا أَخْرِجْنَا مِنْهَا فَإِنْ عُدْنَا فَإِنَّا ظَالِمُونَ (107) قَالَ اخْسَئُوا فِيهَا وَلَا تُكَلِّمُونِ (108) إِنَّهُ كَانَ فَرِيقٌ مِّنْ عِبَادِي يَقُولُونَ رَبَّنَا آمَنَّا فَاغْفِرْ لَنَا وَارْحَمْنَا وَأَنتَ خَيْرُ الرَّاحِمِينَ (109) فَاتَّخَذْتُمُوهُمْ سِخْرِيًّا حَتَّىٰ أَنسَوْكُمْ ذِكْرِي وَكُنتُم مِّنْهُمْ تَضْحَكُونَ (110) إِنِّي جَزَيْتُهُمُ الْيَوْمَ بِمَا صَبَرُوا أَنَّهُمْ هُمُ الْفَائِزُونَ (111) قَالَ كَمْ لَبِثْتُمْ فِي الْأَرْضِ عَدَدَ سِنِينَ (112) قَالُوا لَبِثْنَا يَوْمًا أَوْ بَعْضَ يَوْمٍ فَاسْأَلِ الْعَادِّينَ (113) قَالَ إِن لَّبِثْتُمْ إِلَّا قَلِيلًا ۖ لَّوْ أَنَّكُمْ كُنتُمْ تَعْلَمُونَ (114) أَفَحَسِبْتُمْ أَنَّمَا خَلَقْنَاكُمْ عَبَثًا وَأَنَّكُمْ إِلَيْنَا لَا تُرْجَعُونَ (115) فَتَعَالَى اللَّهُ الْمَلِكُ الْحَقُّ ۖ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ رَبُّ الْعَرْشِ الْكَرِيمِ (116) وَمَن يَدْعُ مَعَ اللَّهِ إِلَٰهًا آخَرَ لَا بُرْهَانَ لَهُ بِهِ فَإِنَّمَا حِسَابُهُ عِندَ رَبِّهِ ۚ إِنَّهُ لَا يُفْلِحُ الْكَافِرُونَ (117) وَقُل رَّبِّ اغْفِرْ وَارْحَمْ وَأَنتَ خَيْرُ الرَّاحِمِينَ (118)
الصفحة Page 349
(105) "Shin, ayõyĩNa ba su kasance anã karanta su a kanku ba sai kuka kasance game da su kunã ƙaryatãwa?"
(106) Suka ce: "Yã Ubangijinmu, shaƙãwamiu ce ta rinjãya a kanmu, kuma mun kasance mutãne ɓatattu."
(107) "Yã Ubangjinmu! Ka fitar da mu daga gare ta, sa'an nan idan mun kõma, to, lalle ne, mũ ne mãsu zãlunci."
(108) Ya ce: "Ku tafi (da wulãkanci) a cikinta. Kada ku yi Mini magana."
(109) Lalle ne waɗansu ƙungiyoyi daga bãyiNa sun kasance sunã cẽwa, "Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni, sai Ka gãfarta mana, kuma Ka yi mana rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu tausayi."
(110) Sai kuka riƙe su lẽburõri har suka mantar da ku ambatõNa kuma kun kasance, daga gare su kuke yin dãriya.
(111) Lalle ne Nĩ Inã sãka musu a yau, sabõda abin da suka yi wa haƙuri. Dõmin lalle ne sũ sũ ne mãsu sãmun babban rabo.
(112) Ya ce: "Nawa kuka zauna a cikin ƙasa na ƙidãyar shẽkaru?"
(113) Suka ce: "Mun zauna a yini ɗaya ko rabin yini, sai ka tambayi mãsu ƙidãyãwa."
(114) Ya ce: "Ba ku zauna ba fãce kaɗan, dã dai kun kasance kunã sani."
(115) "Shin, to, kun yi zaton cẽwa Mun halitta ku ne da wãsa kuma lalle ku, zuwa gare Mu, bã zã ku kõmo ba?"
(116) Allah Mamallaki gaskiya, Yã ɗaukaka. Bãbu abin bautãwa, fãce Shi. Shĩ ne Ubangijin Al'arshi, mai daraja.
(117) Kuma wanda ya kira, tãre da Allah, waɗansu abũbuwan bautãwa na dabam, bã yanã da wani dalĩli game da shĩ (kiran) ba, to hisãbinsa yanã wurin Ubangijinsa kawai. Lalle ne, kãfirai bã su cin nasara.
(118) Kuma ka ce: "Yã Ubangijina! Ka yi gãfara, Ka yi rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu rahama."
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022