(38) Kuma waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu dõmin nũna wa mutãne, kuma bã su yin ĩmãni da Allah, kuma bã su yin ĩmãnida Rãnar Lãhira kuma wanda Shaiɗan ya kasance abõkin haɗi a gare shi, to, yã mũnana ga abõkinhaɗi.
(39) Kuma mẽne ne a kansu, idan sun yi ĩmãni da Allah, kumada Rãnar Lãhira, kuma sun ciyar da abin da Allah Yã azurtã su, kuma Allah Ya kasance, gare su, Masani?
(40) Lalle ne, Allah bã Ya zãluncin gwargwadon nauyin zarra, idan ta kasance alhẽri ce, zai riɓanya ta, kuma Ya kãwo daga gunsa ijãra mai girma.
(41) To, yãyã, idan Mun zo da shaidu daga dukkan al'umma, kuma Muka zo da kai a kan waɗannan, kana mai shaida!
(42) A rãnar nan, waɗanda suka kãfirta kuma suka sãɓã wa Manzo, sunã gũrin dã an baje ƙasa dasu, kuma bã su ɓõye wa Allah wani labãri.
(43) Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kusanci salla alhãli kuwa kuna mãsu mãye, sai kun san abin da kuke faɗa kuma haka idan kuna mãsu janaba, fãce mai ƙẽtare hanya, har ku yi wanka. Kuma idan kun kasance majinyata, ko kuwa a kan tafiya ko kuwa wani daga cikinku, idan ya zo daga kãshi, kõ kuwa kun shãfi mãtã ba ku sãmi ruwa ba, to ku nufi, fuskar ƙasa mai kyau, ku yi shãfa ga fuskokinku da hannuwanku. Lalle ne Allah Yã kasance Mai yãfẽwa Mai gãfara.
(44) Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda aka bai wa rabo daga Littafi, suna sayen ɓata, kuma suna nẽman ku ɓace daga hanya?