(14) Ku yãƙe su, Allah Ya yi musu azabã da hannãyenku, kuma Ya kunyatar da su, kuma Ya taimake ku, kuma Ya warkar da ƙirãzan mutãne mũminai.
(15) Kuma Ya tafĩ da fushin zukãtansu, kuma Ya karɓi tũba a kan wanda Ya so. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.
(16) Kõ kunã zaton a bar ku, tun Allah bai bayyana waɗanda suka yi jihãdi ba daga gare ku, kuma sũ ba su riƙi wani shigeba, baicin Allah da ManzonSa da mũminai? Kuma Allah ne Mai jarrabãwa ga abin da kuke aikatãwa.
(17) Bã ya kasancewa ga mãsu shirki su rãya masallatan Allah, alhãli kuwa sunã mãsu bãyar da shaida a kan rãyukansu da kafirci, waɗannan ayyukansu sun ɓãci, kuma a cikin wutã sũ madawwama
(18) Abin sani kawai, mai rãya masallãtan Allah, shĩ ne wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya tsayar da salla kuma ya bãyar da zakka, kuma bai ji tsõron kõwa ba fãce Allah. To, akwai tsammãnin waɗannan su kasance daga shiryayyu.
(19) Shin, kun sanya shãyar da mahajjata da rãyar da Masallaci Mai alfarma kamar wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya yi jihãɗi a cikin hanyar Allah? Bã su daidaita a wurin Allah. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
(20) Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihãdi, a cikin hanyar Allah, da dũkiyõyinsu, da rãyukansu, sũ ne mafi girma ga daraja, a wurin Allah, kuma waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.