(64) Kõ wãne ne yake fã ra halitta sa'an nan kuma ya mayar da ita, kuma Wãne ne Ya azurta ku daga sama da ƙasa? Ashe, akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? Ka ce: "Ku kãwo dalĩlinku idan kun kasance mãsu gaskiya."
(65) Ka ce: "Bãbu wanda ya san gaibi a cikin sammai da ƙasa fãce Allah. Kuma bã su sansancẽwar a yaushe ne zã a tãyar da su."
(66) Ã'a, saninsu ya kai a cikin Lãhira Ã'a, sunã cikin shakka daga gare ta. Ã'a, sũ da gare ta makãfin zũci ne.
(67) Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Shin idan mun kasance turɓaya, mu da ubanninmu, shin, haƙĩƙa, waɗanda ake fitarwa ne?"
(68) "Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi ga wannan, mũ da ubanninmu, daga gabãnin haka. Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin farko."
(69) Ka ce: "Ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba, yãya ãƙibar mãsu laifi take?"
(70) Kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke ƙullãwa na mãkirci.
(71) Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi (zai auku), idan kun kasance mãsu gaskiya?"
(72) Ka ce: "Akwai fatan sãshen abin da kuke, nẽman gaggãwarsa, ya kasance yã kuturta a gare ku."
(73) Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa Mai falala ne a kanmutãne kuma amma mafi yawansu, bã su gõdẽwa.
(74) Kuma lalle Ubangijinka, haƙĩƙa Yanã sanin abin da ƙirãzansu suke, ɓõyẽwa, da abin da suke hayyanãwa.
(75) Kuma bãbu wata (mas'ala) mai bõyuwa, a cikin sama da ƙasa fãce tanã a cikin littafi bayyananne.
(76) Lalle ne wannan Alƙur'ãni yanã gaya wa Banĩ Isrãĩla mafi yawan abin da sũ suke sãɓa wa jũnansu a ciki.