التكوير   سورة  : At-Takwir


سورة Sura   التكوير   At-Takwir
التكوير At-Takwir
إِذَا الشَّمْسُ كُوِّرَتْ (1) وَإِذَا النُّجُومُ انكَدَرَتْ (2) وَإِذَا الْجِبَالُ سُيِّرَتْ (3) وَإِذَا الْعِشَارُ عُطِّلَتْ (4) وَإِذَا الْوُحُوشُ حُشِرَتْ (5) وَإِذَا الْبِحَارُ سُجِّرَتْ (6) وَإِذَا النُّفُوسُ زُوِّجَتْ (7) وَإِذَا الْمَوْءُودَةُ سُئِلَتْ (8) بِأَيِّ ذَنبٍ قُتِلَتْ (9) وَإِذَا الصُّحُفُ نُشِرَتْ (10) وَإِذَا السَّمَاءُ كُشِطَتْ (11) وَإِذَا الْجَحِيمُ سُعِّرَتْ (12) وَإِذَا الْجَنَّةُ أُزْلِفَتْ (13) عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّا أَحْضَرَتْ (14) فَلَا أُقْسِمُ بِالْخُنَّسِ (15) الْجَوَارِ الْكُنَّسِ (16) وَاللَّيْلِ إِذَا عَسْعَسَ (17) وَالصُّبْحِ إِذَا تَنَفَّسَ (18) إِنَّهُ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ (19) ذِي قُوَّةٍ عِندَ ذِي الْعَرْشِ مَكِينٍ (20) مُّطَاعٍ ثَمَّ أَمِينٍ (21) وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجْنُونٍ (22) وَلَقَدْ رَآهُ بِالْأُفُقِ الْمُبِينِ (23) وَمَا هُوَ عَلَى الْغَيْبِ بِضَنِينٍ (24) وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَيْطَانٍ رَّجِيمٍ (25) فَأَيْنَ تَذْهَبُونَ (26) إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَالَمِينَ (27) لِمَن شَاءَ مِنكُمْ أَن يَسْتَقِيمَ (28) وَمَا تَشَاءُونَ إِلَّا أَن يَشَاءَ اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ (29)
الصفحة Page 586
التكوير At-Takwir
(1) Idan rãna aka shafe haskenta
(2) Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).
(3) Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.
(4) Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.
(5) Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.
(6) Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.
(7) Kuma idan rãyuka aka haɗa su da jikunkunansu.
(8) Kuma idan wadda aka turbuɗe ta da rai aka tambaye ta.
(9) "Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?"
(10) Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).
(11) Kuma idan sama aka fẽɗe ta.
(12) Kuma idan Jahĩm aka hũra ta
(13) Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.
(14) Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).
(15) To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã ba.
(16) Mãsu gudu suna ɓũya.
(17) Da dare idan ya bãyar da bãya.
(18) Da sãfiya idan ta yi lumfashi.
(19) Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.
(20) Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.
(21) Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce.
(22) Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.
(23) Kuma lalle ne, yã gan shi a cikin sararin sama mabayyani.
(24) Kuma shi, ga gaibi bã mai rowa ba ne.
(25) Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.
(26) Shin, a inã zã ku tafi?
(27) Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.
(28) Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.
(29) Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022