لقمان   سورة  : Luqman


سورة Sura   لقمان   Luqman
لقمان Luqman
الم (1) تِلْكَ آيَاتُ الْكِتَابِ الْحَكِيمِ (2) هُدًى وَرَحْمَةً لِّلْمُحْسِنِينَ (3) الَّذِينَ يُقِيمُونَ الصَّلَاةَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَهُم بِالْآخِرَةِ هُمْ يُوقِنُونَ (4) أُولَٰئِكَ عَلَىٰ هُدًى مِّن رَّبِّهِمْ ۖ وَأُولَٰئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ (5) وَمِنَ النَّاسِ مَن يَشْتَرِي لَهْوَ الْحَدِيثِ لِيُضِلَّ عَن سَبِيلِ اللَّهِ بِغَيْرِ عِلْمٍ وَيَتَّخِذَهَا هُزُوًا ۚ أُولَٰئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ مُّهِينٌ (6) وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِ آيَاتُنَا وَلَّىٰ مُسْتَكْبِرًا كَأَن لَّمْ يَسْمَعْهَا كَأَنَّ فِي أُذُنَيْهِ وَقْرًا ۖ فَبَشِّرْهُ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ (7) إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَهُمْ جَنَّاتُ النَّعِيمِ (8) خَالِدِينَ فِيهَا ۖ وَعْدَ اللَّهِ حَقًّا ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ (9) خَلَقَ السَّمَاوَاتِ بِغَيْرِ عَمَدٍ تَرَوْنَهَا ۖ وَأَلْقَىٰ فِي الْأَرْضِ رَوَاسِيَ أَن تَمِيدَ بِكُمْ وَبَثَّ فِيهَا مِن كُلِّ دَابَّةٍ ۚ وَأَنزَلْنَا مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَأَنبَتْنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوْجٍ كَرِيمٍ (10) هَٰذَا خَلْقُ اللَّهِ فَأَرُونِي مَاذَا خَلَقَ الَّذِينَ مِن دُونِهِ ۚ بَلِ الظَّالِمُونَ فِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ (11)
الصفحة Page 411
لقمان Luqman
(1) A. L̃. M̃.
(2) Waɗancan ãyõyin Littãfin ne mai hikima.
(3) Shiriya da rahama ne ga mãsu kyautatawa.
(4) Waɗanda ke tsai da salla kuma sunã ɓãyar da zakka kuma sũ, sunã yin ĩmãnin yaƙĩni, ga lãhira.
(5) Waɗannan sunã a kan shiriya ta daga Ubangijinsu kuma waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
(6) Kuma akwai daga cikin mutãne wanda ke sayen tãtsuniyõyi dõmin ya ɓatar da mutãne daga hanyar Allah, bã da wani ilmi ba, kuma ya riƙe ta abin izgili! Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa.
(7) Kuma idan an karanta ãyõyinMu a gare shi, sai ya jũya bãya, yanã mai girman kai, kamar dai bai saurãre su ba kamar dai akwai wanĩ danni a kan kunnuwansa! To, ka yi masa bushãra da azãba mai raɗaɗi.
(8) Lalle, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljannar ni'ima.
(9) Sunã dawwama a cikinsu Allah Yã yi alkawarin, Ya tabbatar da shi. Kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.
(10) (Allah) Ya halitta sammai, bã da ginshiƙi wanda kuke gani ba, kuma Yã jẽfa duwatsu mãsu kafuwa a cikin ƙasã, dõmin kada ta karkata da ku kuma Ya wãtsa daga kowanc irin dabba a cikinta, kuma Mun saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka tsirar a cikinta, daga kõwane nau'i biyu (nami; i da mace) mai ban sha'awa.
(11) Wannan shĩ ne halittar Allah. To ku nũna mini, "Mẽne ne waɗanan da ba Shi ba suka halitta? Ã'a, azzalumai sunã a cikin ɓata bayyananna."
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022