العنكبوت   سورة  : Al-Ankaboot


سورة Sura   العنكبوت   Al-Ankaboot
وَلَمَّا جَاءَتْ رُسُلُنَا إِبْرَاهِيمَ بِالْبُشْرَىٰ قَالُوا إِنَّا مُهْلِكُو أَهْلِ هَٰذِهِ الْقَرْيَةِ ۖ إِنَّ أَهْلَهَا كَانُوا ظَالِمِينَ (31) قَالَ إِنَّ فِيهَا لُوطًا ۚ قَالُوا نَحْنُ أَعْلَمُ بِمَن فِيهَا ۖ لَنُنَجِّيَنَّهُ وَأَهْلَهُ إِلَّا امْرَأَتَهُ كَانَتْ مِنَ الْغَابِرِينَ (32) وَلَمَّا أَن جَاءَتْ رُسُلُنَا لُوطًا سِيءَ بِهِمْ وَضَاقَ بِهِمْ ذَرْعًا وَقَالُوا لَا تَخَفْ وَلَا تَحْزَنْ ۖ إِنَّا مُنَجُّوكَ وَأَهْلَكَ إِلَّا امْرَأَتَكَ كَانَتْ مِنَ الْغَابِرِينَ (33) إِنَّا مُنزِلُونَ عَلَىٰ أَهْلِ هَٰذِهِ الْقَرْيَةِ رِجْزًا مِّنَ السَّمَاءِ بِمَا كَانُوا يَفْسُقُونَ (34) وَلَقَد تَّرَكْنَا مِنْهَا آيَةً بَيِّنَةً لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ (35) وَإِلَىٰ مَدْيَنَ أَخَاهُمْ شُعَيْبًا فَقَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللَّهَ وَارْجُوا الْيَوْمَ الْآخِرَ وَلَا تَعْثَوْا فِي الْأَرْضِ مُفْسِدِينَ (36) فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَتْهُمُ الرَّجْفَةُ فَأَصْبَحُوا فِي دَارِهِمْ جَاثِمِينَ (37) وَعَادًا وَثَمُودَ وَقَد تَّبَيَّنَ لَكُم مِّن مَّسَاكِنِهِمْ ۖ وَزَيَّنَ لَهُمُ الشَّيْطَانُ أَعْمَالَهُمْ فَصَدَّهُمْ عَنِ السَّبِيلِ وَكَانُوا مُسْتَبْصِرِينَ (38)
الصفحة Page 400
(31) Kuma a lõkacin da ManzanninMu suka jẽ wa Ibrãhĩm da bushãra suka ce: "Lalle mu mãsu halaka mutãnen, wannan alƙarya ne. Lalle mutãnenta sun kasance mãsu zãlunci."
(32) Ya ce: "Lalle akwai Lũɗu a cikinta!" Suka ce: "Mũ ne mafiya sani ga waɗanda suke a cikinta, lalle munã tsĩrar da shi da mutãnensa, fãce fa mãtarsa ta kasance a cikin mãsu wanzuwa."
(33) Kuma a lõkacin da ManzanninMu suka je wa Lũɗu ya ɓãta rai sabõda su, kuma yã ƙuntata ga kirji sabõda su. Kuma suka ce: "Kada ka ji tsõro kuma kada ka yi baƙin ciki lalle mũ mãsu tsĩrar da kai ne da iyãlanka, fãce dai matarka ta kasance daga mãsu wanzuwa.
(34) "Lalle mũ, mãsu saukar da azãba ne daga sama a kan mutãnen wannan alƙarya sabõda abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci."
(35) Kuma lalle Mun bar wata ãyã bayyananna daga gare ta ga mutãne mãsu hankalta.
(36) Kuma zuwa ga Madyana, Mun aika ɗan'uwansu shu'aibu, sai ya ce: "Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah kuma ku yi fatan (rahamar) Rãnar Lãhira, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasã, alhãli kuwa kunã mãsu lãlãtarwa."
(37) Sai suka ƙaryata shi, sabõda haka tsãwa ta kãmã su, dõmin haka suka wãyi gari sunã guggurfãne.
(38) Da Ãdawa da Samũdãwa alhãli kuwa lalle alãmun azãba sun bayyana a gare su daga gidãjensu kuma Shaiɗan ya ƙawãta musu ayyukansu, sabõda haka ya kange su daga hanyar Allah, kuma sun kasance mãsu basĩra!
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022