الحشر   سورة  : Al-Hashr


سورة Sura   الحشر   Al-Hashr
لَّا تَجِدُ قَوْمًا يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ يُوَادُّونَ مَنْ حَادَّ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَلَوْ كَانُوا آبَاءَهُمْ أَوْ أَبْنَاءَهُمْ أَوْ إِخْوَانَهُمْ أَوْ عَشِيرَتَهُمْ ۚ أُولَٰئِكَ كَتَبَ فِي قُلُوبِهِمُ الْإِيمَانَ وَأَيَّدَهُم بِرُوحٍ مِّنْهُ ۖ وَيُدْخِلُهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ۚ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ ۚ أُولَٰئِكَ حِزْبُ اللَّهِ ۚ أَلَا إِنَّ حِزْبَ اللَّهِ هُمُ الْمُفْلِحُونَ (22)
الحشر Al-Hashr
سَبَّحَ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۖ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ (1) هُوَ الَّذِي أَخْرَجَ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ مِن دِيَارِهِمْ لِأَوَّلِ الْحَشْرِ ۚ مَا ظَنَنتُمْ أَن يَخْرُجُوا ۖ وَظَنُّوا أَنَّهُم مَّانِعَتُهُمْ حُصُونُهُم مِّنَ اللَّهِ فَأَتَاهُمُ اللَّهُ مِنْ حَيْثُ لَمْ يَحْتَسِبُوا ۖ وَقَذَفَ فِي قُلُوبِهِمُ الرُّعْبَ ۚ يُخْرِبُونَ بُيُوتَهُم بِأَيْدِيهِمْ وَأَيْدِي الْمُؤْمِنِينَ فَاعْتَبِرُوا يَا أُولِي الْأَبْصَارِ (2) وَلَوْلَا أَن كَتَبَ اللَّهُ عَلَيْهِمُ الْجَلَاءَ لَعَذَّبَهُمْ فِي الدُّنْيَا ۖ وَلَهُمْ فِي الْآخِرَةِ عَذَابُ النَّارِ (3)
الصفحة Page 545
(22) Bã zã ka sãmi mutãne mãsu yin ĩmãni da Allah da RãnarLãhira sunã sõyayya da wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa ba, kõ dã sun kasance ubanninsu ne, kõ ɗiyansu kõ 'yan'uwansu, ko danginsu. waɗannan Allah Yã rubuta ĩmãni a cikin zukãtansu, kuma Yã ƙarfafa su da wani rũhi daga gare Shi, kuma zai shigar da su a gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu. Allah Yã yarda da su, kuma sun yarda da Shi. Waɗannan ƙungiyar Allah ne. To, lalle ƙungiyar Allah sũ ne mãsu babban rabo.
الحشر Al-Hashr
(1) Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasã ya yi tasbihi ga Allah, alhãli kuwa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.
(2) Shĩ ne wanda Ya fitar da waɗanda suka kãfirta daga Mazõwa Littãfi, daga gidãjẽnsu da kõra ta farko. Ba ku yi zaton sunã fita ba, kuma sun tabbata cẽwa gãnuwõwinsu mãsu tsare su ne daga Allah, sai Allah Ya jẽ musu daga wajen da ba su yi zato ba, kuma Ya jẽfa tsõro a cikin zukãtansu, sunã rushe gidãjensu da hannãyensu da kuma hannãyen mũminai. To, ku lũra fa, ya mãsu basĩrõri.
(3) Kuma ba dõmin Allah Ya rubuta musu kõrar ba, dã Ya azabta su a cikin dũniya, kuma a Lãhira sunã da azãbar wutã.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022