النبإ   سورة  : An-Naba


سورة Sura   النبإ   An-Naba
إِنَّ لِلْمُتَّقِينَ مَفَازًا (31) حَدَائِقَ وَأَعْنَابًا (32) وَكَوَاعِبَ أَتْرَابًا (33) وَكَأْسًا دِهَاقًا (34) لَّا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا كِذَّابًا (35) جَزَاءً مِّن رَّبِّكَ عَطَاءً حِسَابًا (36) رَّبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا الرَّحْمَٰنِ ۖ لَا يَمْلِكُونَ مِنْهُ خِطَابًا (37) يَوْمَ يَقُومُ الرُّوحُ وَالْمَلَائِكَةُ صَفًّا ۖ لَّا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنْ أَذِنَ لَهُ الرَّحْمَٰنُ وَقَالَ صَوَابًا (38) ذَٰلِكَ الْيَوْمُ الْحَقُّ ۖ فَمَن شَاءَ اتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِ مَآبًا (39) إِنَّا أَنذَرْنَاكُمْ عَذَابًا قَرِيبًا يَوْمَ يَنظُرُ الْمَرْءُ مَا قَدَّمَتْ يَدَاهُ وَيَقُولُ الْكَافِرُ يَا لَيْتَنِي كُنتُ تُرَابًا (40)
النازعات An-Naazi'aat
وَالنَّازِعَاتِ غَرْقًا (1) وَالنَّاشِطَاتِ نَشْطًا (2) وَالسَّابِحَاتِ سَبْحًا (3) فَالسَّابِقَاتِ سَبْقًا (4) فَالْمُدَبِّرَاتِ أَمْرًا (5) يَوْمَ تَرْجُفُ الرَّاجِفَةُ (6) تَتْبَعُهَا الرَّادِفَةُ (7) قُلُوبٌ يَوْمَئِذٍ وَاجِفَةٌ (8) أَبْصَارُهَا خَاشِعَةٌ (9) يَقُولُونَ أَإِنَّا لَمَرْدُودُونَ فِي الْحَافِرَةِ (10) أَإِذَا كُنَّا عِظَامًا نَّخِرَةً (11) قَالُوا تِلْكَ إِذًا كَرَّةٌ خَاسِرَةٌ (12) فَإِنَّمَا هِيَ زَجْرَةٌ وَاحِدَةٌ (13) فَإِذَا هُم بِالسَّاهِرَةِ (14) هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ مُوسَىٰ (15)
الصفحة Page 583
(31) Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo.
(32) Lambuna da inabõbi.
(33) Da cikakkun 'yammata, tsãrar jũna.
(34) Da hinjãlan giya cikakku.
(35) Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa.
(36) Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa.
(37) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi.
(38) Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai.
(39) Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa.
(40) Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!"
النازعات An-Naazi'aat
(1) Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi.
(2) Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi.
(3) Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.
(4) Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umurnin Allah) kamar suna tsẽre.
(5) Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni.
(6) Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa.
(7) Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye.
(8) Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne.
(9) Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu.
(10) Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu?
(11) "Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?"
(12) Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!"
(13) To, ita kam, tsãwa guda kawai ce.
(14) Sai kawai gã su a bãyan ƙasa.
(15) Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022