المرسلات   سورة  : Al-Mursalaat


سورة Sura   المرسلات   Al-Mursalaat
أَلَمْ نَخْلُقكُّم مِّن مَّاءٍ مَّهِينٍ (20) فَجَعَلْنَاهُ فِي قَرَارٍ مَّكِينٍ (21) إِلَىٰ قَدَرٍ مَّعْلُومٍ (22) فَقَدَرْنَا فَنِعْمَ الْقَادِرُونَ (23) وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (24) أَلَمْ نَجْعَلِ الْأَرْضَ كِفَاتًا (25) أَحْيَاءً وَأَمْوَاتًا (26) وَجَعَلْنَا فِيهَا رَوَاسِيَ شَامِخَاتٍ وَأَسْقَيْنَاكُم مَّاءً فُرَاتًا (27) وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (28) انطَلِقُوا إِلَىٰ مَا كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَ (29) انطَلِقُوا إِلَىٰ ظِلٍّ ذِي ثَلَاثِ شُعَبٍ (30) لَّا ظَلِيلٍ وَلَا يُغْنِي مِنَ اللَّهَبِ (31) إِنَّهَا تَرْمِي بِشَرَرٍ كَالْقَصْرِ (32) كَأَنَّهُ جِمَالَتٌ صُفْرٌ (33) وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (34) هَٰذَا يَوْمُ لَا يَنطِقُونَ (35) وَلَا يُؤْذَنُ لَهُمْ فَيَعْتَذِرُونَ (36) وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (37) هَٰذَا يَوْمُ الْفَصْلِ ۖ جَمَعْنَاكُمْ وَالْأَوَّلِينَ (38) فَإِن كَانَ لَكُمْ كَيْدٌ فَكِيدُونِ (39) وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (40) إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي ظِلَالٍ وَعُيُونٍ (41) وَفَوَاكِهَ مِمَّا يَشْتَهُونَ (42) كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئًا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ (43) إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ (44) وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (45) كُلُوا وَتَمَتَّعُوا قَلِيلًا إِنَّكُم مُّجْرِمُونَ (46) وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (47) وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ارْكَعُوا لَا يَرْكَعُونَ (48) وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (49) فَبِأَيِّ حَدِيثٍ بَعْدَهُ يُؤْمِنُونَ (50)
الصفحة Page 581
(20) Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba.
(21) Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce.
(22) Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna.
(23) Sa'an nan, Muka nũna iyãwarMu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa.
(24) Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
(25) Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba.
(26) Ga rãyayyu da matattu,
(27) Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi?
(28) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
(29) Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi!
(30) Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku.
(31) Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta.
(32) Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye.
(33) Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe.
(34) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
(35) Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba.
(36) Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari.
(37) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
(38) Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko.
(39) To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita.
(40) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
(41) Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari.
(42) Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari.
(43) (A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa."
(44) Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
(45) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
(46) (Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne."
(47) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
(48) Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba."
(49) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
(50) To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022