الإسراء   سورة  : Al-Israa


سورة Sura   الإسراء   Al-Israa
ذَٰلِكَ مِمَّا أَوْحَىٰ إِلَيْكَ رَبُّكَ مِنَ الْحِكْمَةِ ۗ وَلَا تَجْعَلْ مَعَ اللَّهِ إِلَٰهًا آخَرَ فَتُلْقَىٰ فِي جَهَنَّمَ مَلُومًا مَّدْحُورًا (39) أَفَأَصْفَاكُمْ رَبُّكُم بِالْبَنِينَ وَاتَّخَذَ مِنَ الْمَلَائِكَةِ إِنَاثًا ۚ إِنَّكُمْ لَتَقُولُونَ قَوْلًا عَظِيمًا (40) وَلَقَدْ صَرَّفْنَا فِي هَٰذَا الْقُرْآنِ لِيَذَّكَّرُوا وَمَا يَزِيدُهُمْ إِلَّا نُفُورًا (41) قُل لَّوْ كَانَ مَعَهُ آلِهَةٌ كَمَا يَقُولُونَ إِذًا لَّابْتَغَوْا إِلَىٰ ذِي الْعَرْشِ سَبِيلًا (42) سُبْحَانَهُ وَتَعَالَىٰ عَمَّا يَقُولُونَ عُلُوًّا كَبِيرًا (43) تُسَبِّحُ لَهُ السَّمَاوَاتُ السَّبْعُ وَالْأَرْضُ وَمَن فِيهِنَّ ۚ وَإِن مِّن شَيْءٍ إِلَّا يُسَبِّحُ بِحَمْدِهِ وَلَٰكِن لَّا تَفْقَهُونَ تَسْبِيحَهُمْ ۗ إِنَّهُ كَانَ حَلِيمًا غَفُورًا (44) وَإِذَا قَرَأْتَ الْقُرْآنَ جَعَلْنَا بَيْنَكَ وَبَيْنَ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِالْآخِرَةِ حِجَابًا مَّسْتُورًا (45) وَجَعَلْنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ أَكِنَّةً أَن يَفْقَهُوهُ وَفِي آذَانِهِمْ وَقْرًا ۚ وَإِذَا ذَكَرْتَ رَبَّكَ فِي الْقُرْآنِ وَحْدَهُ وَلَّوْا عَلَىٰ أَدْبَارِهِمْ نُفُورًا (46) نَّحْنُ أَعْلَمُ بِمَا يَسْتَمِعُونَ بِهِ إِذْ يَسْتَمِعُونَ إِلَيْكَ وَإِذْ هُمْ نَجْوَىٰ إِذْ يَقُولُ الظَّالِمُونَ إِن تَتَّبِعُونَ إِلَّا رَجُلًا مَّسْحُورًا (47) انظُرْ كَيْفَ ضَرَبُوا لَكَ الْأَمْثَالَ فَضَلُّوا فَلَا يَسْتَطِيعُونَ سَبِيلًا (48) وَقَالُوا أَإِذَا كُنَّا عِظَامًا وَرُفَاتًا أَإِنَّا لَمَبْعُوثُونَ خَلْقًا جَدِيدًا (49)
الصفحة Page 286
(39) Wancan yãnã daga abin da Ubangijinka Ya yi wahayi zuwa gare ka na hikima. Kuma kada ka sanya wani abin bautãwa na daban tãre da Allah har a jẽfa ka a cikin Jahannama kanã wanda ake zargi, wanda ake tunkuɗẽwa
(40) Shin fa, Ubangijinku Ya zãɓe ku da ɗiya maza ne, kuma Ya riƙi 'ya'ya mãta daga malã'iku? Lalle ne kũ, haƙĩƙa, kunã faɗar magana mai girma!
(41) Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarrafa bayãni a cikin wannan Alƙur'ãni dõmin su yi tunãni, kuma bã ya ƙãra musu kõme fãce gudu.
(42) Ka ce: "Dã akwai waɗansu abũbuwan bautãwa tãre da shi, kamar yadda suka faɗa, a lõkacin, dã (abũbuwan bautãwar) sun nẽmi wata hanya zuwa ga Ma'abũcin Al'arshi."
(43) TsarkinSa yã tabbata kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke faɗã, ɗaukaka mai girma.
(44) Sammai bakwai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sunã yi Masa tasbĩhi. Kuma bãbu wani abu fãce yanã tasbĩhi game da gõde Masa, kuma amma ba ku fahimtar tasbĩhinsu. Lalle ne shĩ, Ya kasance Mai haƙuri ne, Mai gãfara.
(45) Kuma idan ka karanta Alƙur'ani, sai Mu sanya a tsakãninka da tsakanin waɗanda bã su yin ĩmãni da Lãhira wani shãmaki mai suturcẽwa.
(46) Kuma Mu sanya marufai a kan zukãtansu dõmin kada su fahimce shi, da, wani nauyi a cikin kunnuwansu, kuma idan ka ambaci Ubangijinka, a cikin Alƙur'ãni shĩ kaɗai, sai su jũya a kan bayayyakinsu dõmin gudu.
(47) Mũ ne Mafi sani game da abin da suke saurãre da shi a lõkacin da suke yin saurãren zuwa gare ka, kuma a lõkacin da suke mãsu gãnãwa a tsakãninsu a lõkacin da azzãlumai suke cẽwa, "Bã ku biyar kõwa fãce wani namiji sihirtacce."
(48) Ka dũba yadda suka buga maka misãlai, sai suka ɓace bã su iya sãmun hanya.
(49) Kuma suka ce: "Shin, idan mun kasance ƙasũsuwa da, niƙaƙƙun gaɓãɓuwa ashe, lalle ne mũ haƙĩƙa, waɗanda ake tãyarwa ne a wata halitta sãbuwa?"
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022