الرعد   سورة  : Ar-Ra'd


سورة Sura   الرعد   Ar-Ra'd
الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ طُوبَىٰ لَهُمْ وَحُسْنُ مَآبٍ (29) كَذَٰلِكَ أَرْسَلْنَاكَ فِي أُمَّةٍ قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِهَا أُمَمٌ لِّتَتْلُوَ عَلَيْهِمُ الَّذِي أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ وَهُمْ يَكْفُرُونَ بِالرَّحْمَٰنِ ۚ قُلْ هُوَ رَبِّي لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَإِلَيْهِ مَتَابِ (30) وَلَوْ أَنَّ قُرْآنًا سُيِّرَتْ بِهِ الْجِبَالُ أَوْ قُطِّعَتْ بِهِ الْأَرْضُ أَوْ كُلِّمَ بِهِ الْمَوْتَىٰ ۗ بَل لِّلَّهِ الْأَمْرُ جَمِيعًا ۗ أَفَلَمْ يَيْأَسِ الَّذِينَ آمَنُوا أَن لَّوْ يَشَاءُ اللَّهُ لَهَدَى النَّاسَ جَمِيعًا ۗ وَلَا يَزَالُ الَّذِينَ كَفَرُوا تُصِيبُهُم بِمَا صَنَعُوا قَارِعَةٌ أَوْ تَحُلُّ قَرِيبًا مِّن دَارِهِمْ حَتَّىٰ يَأْتِيَ وَعْدُ اللَّهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ لَا يُخْلِفُ الْمِيعَادَ (31) وَلَقَدِ اسْتُهْزِئَ بِرُسُلٍ مِّن قَبْلِكَ فَأَمْلَيْتُ لِلَّذِينَ كَفَرُوا ثُمَّ أَخَذْتُهُمْ ۖ فَكَيْفَ كَانَ عِقَابِ (32) أَفَمَنْ هُوَ قَائِمٌ عَلَىٰ كُلِّ نَفْسٍ بِمَا كَسَبَتْ ۗ وَجَعَلُوا لِلَّهِ شُرَكَاءَ قُلْ سَمُّوهُمْ ۚ أَمْ تُنَبِّئُونَهُ بِمَا لَا يَعْلَمُ فِي الْأَرْضِ أَم بِظَاهِرٍ مِّنَ الْقَوْلِ ۗ بَلْ زُيِّنَ لِلَّذِينَ كَفَرُوا مَكْرُهُمْ وَصُدُّوا عَنِ السَّبِيلِ ۗ وَمَن يُضْلِلِ اللَّهُ فَمَا لَهُ مِنْ هَادٍ (33) لَّهُمْ عَذَابٌ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۖ وَلَعَذَابُ الْآخِرَةِ أَشَقُّ ۖ وَمَا لَهُم مِّنَ اللَّهِ مِن وَاقٍ (34)
الصفحة Page 253
(29) Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata aiki nagari, farin ciki yã tabbata a gare su, da kyakkyawar makõma.
(30) Kamar wancan ne Muka aika ka a cikin al'umma wanda take waɗansu al'ummai sun shũɗe daga gabaninta, dõmin ka karanta musu abin da Muka yi wahayi zuwa a gare ka, alhãli kuwa sũ, sunãkãfirta da Rahaman. Ka ce: "Shi ne Ubangijĩna, bãbu abin, bautãwa fãce Shi, a gare Shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi tũbãta take."
(31) Kuma dã lalle an saukar da wani littafi abin karatu wanda ake tafiyar da duwãtsu game da shi, kõ kuma aka yanyanke ƙasa da shi, ko kuwa aka yi magana da matattu da shi (dã ba su yi ĩmãni ba). Ã'a ga Allah al'amari yake gabã ɗaya! Shin fa, waɗanda suka yi ĩmãni ba su yanke tsammãni ba da cẽwa da Allah Yã so, dã Yã shiryar da mutãne gabã ɗaya? Kuma waɗanda suka yi kãfirci ba zã su gushe ba wata masĩfa tanã samun su sabõda abin da suka aikata, kõ kuwa ka saukã kusa da gidãjẽnsu, har wa'adin Allah ya zo. Kuma lalle ne Allah bã ya sãɓã wa lõkacin alkawari.
(32) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili da Manzanni kãfinka, sai Na yi jinkiri ga waɗanda suka kãfirta, sa'an nan Na kãma su. To, yãya uƙũbãta take?
(33) Shin fa, wanda shĩ Yake tsaye a kan kõwane rai game da abin da ya tanada (zai zama kamar wanda ba haka ba)? Kuma suka sanya abõkan tãrayya ga Allah! Ka ce: "Ku ambaci sũnãyensu."Ko kunã bai wa Allah lãbãri ne game da abin da bai sani ba a cikin ƙasa? Kõ da bayyananniyar magana kuke yin shirka, (banda a cikin zũciya)? Ã'a, an dai ƙawãta wa waɗanda suka kafirta mãkircinsu kuma an kange su daga hanya. Kuma wanda Allah Ya ɓatar to, bãbu wani mai shiryarwa a gare shi!"
(34) Sunã da wata azãba a cikin rãyuwar dũniya, kuma haƙĩƙa azãbar Lãhira ce mafi tsanani kuma bãbu wani mai tsare su daga Allah.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022