(5) Ba su da wani ilmi game da wannan magana, kuma iyãyensu bã su da shi, abin da ke fita daga bãkunansu ya girma ga ya zama kalmar faɗa! Ba su faɗan kõme fãce ƙarya.
(6) To, kã yi kusa ka halaka ranka a gurabbansu, wai dõmin ba su yi ĩmãni da wannan lãbãri ba sabõda baƙin ciki.
(7) Lalle ne Mũ, Mun sanya abin da ke kan ƙasa wata ƙawa ce gare ta, dõmin Mu jarraba su; wanne daga cikinsu zai zama mafi kyau ga aiki.
(8) Kuma lalle Mũ, Mãsu sanya abin da ke a kanta (ya zama) turɓãya ƙeƙasasshiya ne.
(9) Ko kuwa kã yi zaton cẽwa ma'abũta kõgo da allo sun kasance abin mãmãki daga ãyõyin Allah?
(10) A lõkacin da samarin suka tattara zuwa ga kõgon, sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka bã mu wata rahama daga gare Ka, kuma Ka sauƙaƙe mana (sãmun) shiriya daga al'amarinmu."
(11) Sai Muka yi dũka a kan kunnunwansu, a cikin kõgon, shẽkaru mãsu yawa.
(12) Sa'an nan Muka tãyar da su, dõmin Mu san wane ɗayan ƙungiyõyin biyu suka fi lissãfi ga abin da suka zauna na lõkacin.
(13) Mu ne ke jẽranta maka lãbãrinsu da gaskiya. Lalle ne sũ, waɗansu samãri ne. Sun yi ĩmãni da Ubangijinsu, kuma Muka ƙãra musu wata shiriya.
(14) Kuma Muka ɗaure a kan zukãtansu, a lõkacin da suka tsayu, sa'an nan suka ce: "Ubangijinmu Shĩ ne Ubangijin sammai daƙasa. Bã zã mu kirãyi waninSa abin bautawa ba. (Idan mun yi haka) lalle ne, haƙĩƙa, mun faɗi abin da ya ƙẽtare haddi a sa'an nan."
(15) "Ga waɗannan mutãnenmu sun riƙi waninSa abin bautãwa! Don me bã su zuwa da wata hujja bayyananna a kansu (waɗanda ake bautawar)? To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙãga ƙarya ga Allah?"