(43) Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.
(44) Sa'an nan kuma Muka aika da ManzanninMu jẽre a kõda yaushe Manzon wata al'umma ya jẽ mata, sai su ƙaryata shi, sabõda haka Muka biyar da sãshensu ga sãshe, kuma Muka sanya su lãbãrun hĩra. To, nĩsa ya tabbata ga mutãne (waɗanda) bã su yin ĩmãni!
(45) Sa'an nan kuma Muka aika Mũsã da ɗan'uwansa Hãrũna, game da ãyõyinMu da, dalĩli bayyananne.
(46) Zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka kangara, alhãli sun kasance mutãne ne marinjãya.
(47) Sai suka ce: "Shin, zã Mu yi ĩmãni sabõda wasu mutãne biyu misãlinmu, alhãli kuwa mutãnensu a gare mu, mãsu bauta ne."
(48) Sai suka ƙaryata su sabõda haka suka kasance halakakku.
(49) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi tsammaninsu zã su shiryu.
(50) Kuma Mun sanya ¦an Maryama, shi da uwarsa wata ãyã Kuma Muka tattara su zuwa ga wani tsauni ma'abũcin natsuwa da marẽmari.
(51) Yã ku Manzanni! Ku ci daga abũbuwa mãsu dãɗi kuma ku aikata aikin ƙwarai. Lalle Nĩga abin da kuke aikatãwa, Masani ne.
(52) Kuma lalle ne, wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Nĩ, Ubangijinku ne, sai ku bĩ Ni da taƙawa.
(53) Sai (al'ummar) suka yanyanke al'amarinsu a tsakãninsu guntu-guntu, kõwace ƙungiya sunã mãsu farin ciki da abin da yake a gare su.
(54) To, ka bar su a cikin ɓatarsu har a wani lõkaci.
(55) Shin, sunã zaton cẽwa abin da Muke taimakon su da shi daga dũkiya da ɗiya,
(56) Munã yi musu gaggãwa ne a cikin alhẽrõri?
(57) Lalle ne waɗanda suke mãsu sauna sabo da tsõron Ubangijinsu,
(58) Da waɗanda suke, game da ãyõyin Ubangijinsu sunã ĩmãni,
(59) Da waɗanda suke game da Ubangijinsu bã su yin shirki,