نوح   سورة  : Nooh


سورة Sura   نوح   Nooh
فَلَا أُقْسِمُ بِرَبِّ الْمَشَارِقِ وَالْمَغَارِبِ إِنَّا لَقَادِرُونَ (40) عَلَىٰ أَن نُّبَدِّلَ خَيْرًا مِّنْهُمْ وَمَا نَحْنُ بِمَسْبُوقِينَ (41) فَذَرْهُمْ يَخُوضُوا وَيَلْعَبُوا حَتَّىٰ يُلَاقُوا يَوْمَهُمُ الَّذِي يُوعَدُونَ (42) يَوْمَ يَخْرُجُونَ مِنَ الْأَجْدَاثِ سِرَاعًا كَأَنَّهُمْ إِلَىٰ نُصُبٍ يُوفِضُونَ (43) خَاشِعَةً أَبْصَارُهُمْ تَرْهَقُهُمْ ذِلَّةٌ ۚ ذَٰلِكَ الْيَوْمُ الَّذِي كَانُوا يُوعَدُونَ (44)
نوح Nooh
إِنَّا أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوْمِهِ أَنْ أَنذِرْ قَوْمَكَ مِن قَبْلِ أَن يَأْتِيَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ (1) قَالَ يَا قَوْمِ إِنِّي لَكُمْ نَذِيرٌ مُّبِينٌ (2) أَنِ اعْبُدُوا اللَّهَ وَاتَّقُوهُ وَأَطِيعُونِ (3) يَغْفِرْ لَكُم مِّن ذُنُوبِكُمْ وَيُؤَخِّرْكُمْ إِلَىٰ أَجَلٍ مُّسَمًّى ۚ إِنَّ أَجَلَ اللَّهِ إِذَا جَاءَ لَا يُؤَخَّرُ ۖ لَوْ كُنتُمْ تَعْلَمُونَ (4) قَالَ رَبِّ إِنِّي دَعَوْتُ قَوْمِي لَيْلًا وَنَهَارًا (5) فَلَمْ يَزِدْهُمْ دُعَائِي إِلَّا فِرَارًا (6) وَإِنِّي كُلَّمَا دَعَوْتُهُمْ لِتَغْفِرَ لَهُمْ جَعَلُوا أَصَابِعَهُمْ فِي آذَانِهِمْ وَاسْتَغْشَوْا ثِيَابَهُمْ وَأَصَرُّوا وَاسْتَكْبَرُوا اسْتِكْبَارًا (7) ثُمَّ إِنِّي دَعَوْتُهُمْ جِهَارًا (8) ثُمَّ إِنِّي أَعْلَنتُ لَهُمْ وَأَسْرَرْتُ لَهُمْ إِسْرَارًا (9) فَقُلْتُ اسْتَغْفِرُوا رَبَّكُمْ إِنَّهُ كَانَ غَفَّارًا (10)
الصفحة Page 570
(40) Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne.
(41) Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba.
(42) Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita).
(43) Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa.
(44) Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa.)
نوح Nooh
(1) Lalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cẽwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu.
(2) Ya ce: "Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa."
(3) "Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõronSa, kuma ku bĩ ni."
(4) "Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci)."
(5) Nũhu) ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini."
(6) "To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni)."
(7) "Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai."
(8) "Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane."
(9) "Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri."
(10) "Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne."
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022