(15) Lalle, haƙĩƙa, akwai ãyã ga saba'ãwa a cikin mazauninsu: gõnakin lambu biyu, dama da hagu. "Ku ci daga arzikin Ubangijinku, kuma ku yi gõdiya gare shi. Gari mai dãɗin zama, da Ubangiji Mai gãfara."
(16) Sai suka bijire sabõda haka Muka saki Mãlãlin Arimi (dam) a kansu, kuma Muka musanya musu gõnakinsu biyu da waɗansu gõnaki biyu mãsu 'ya'yan itãce kaɗan: talãkiya da gõriba da wani abu na magarya kaɗan.
(17) Wancan, da shi Muka yi musu sakamako sabõda kãfircinsu. Kuma lalle, bã Mu yi wa kõwa irin wannan sakamako, fãce kafirai.
(18) Kuma Muka sanya, a tsakaninsu da tsakãnin garũruwan da Muka Sanya albarka a cikinsu, waɗansu garũruwa mãsuganin jũna kuma Muka ƙaddara tafiya a cikinsu, "Ku yi tafiya a cikinsu, darũruwa da rãnaiku, kunã amintattu."
(19) Sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka nĩsantar da tsakãnin tafiyõyinmu," kuma suka zãlunci kansu, sabõda haka Muka sanya su lãbãran hĩra kuma Muka kekkẽce su kõwace, irin kekkẽcewa. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai yawan haƙuri, mai yawan gõdiya.
(20) Kuma lalle, haƙĩƙa, Iblĩs ya gaskata zatonsa a kansu, sai suka bi shi fãce wani ɓangare na mũminai.
(21) Kuma bã ya da wani dalĩli a kansu fãce dai dõmin Mu san wanda yake yin ĩmãni da Lãhira daga wanda yake a cikin shakka daga gare ta. Kuma Ubangijinka, a kan kõme, Mai tsaro ne.
(22) Ka ce: "Ku kirãyi waɗanda kuka riya (cẽwa abũbuwan bautãwa ne) baicin Allah, bã su Mallakar ma'aunin zarra a cikin sammai, kuma bã su Mallakarsa a cikin ƙasa kuma bã su da wani rabon tãrẽwa a cikinsu (sammai da ƙasa), kuma bã Shi da wani mataimaki daga gare su.