(94) Ka ce: "Idan Gidan Lãhira ya kasance sabõda ku, a wurin Allah keɓe bã da sauran mutãne ba, to, ku yi gũrin mutuwa, idan kun kasance mãsu gaskiya."
(95) Kuma bã zã su yi gũrinta bahar abada sabõda abin da hannayensu, suka gabãtar. Kuma Allah Masani ne ga azzãlumai.
(96) Kuma lalle ne, zã ka sãme su mafiya kwaɗayin mutãne a kan rãyuwa, kuma sũ ne mafiya kwaɗayin rãyuwa daga waɗanda suka yi shirka. ¦ayansu yana son dã zã a rãyar da shi shekara dubu, kuma bã ya zama mai nĩsantar da shi daga azãba dõmin an rãyar da shi. Kuma Allah, Mai gani ne ga abin da suke aikatãwa.
(97) Ka ce: Wanda ya kasance maƙiyi ga Jibirilu, to, lalle ne shi ya saukar da shi a kan zũciyarka da izinin Allah, yana mai gaskatãwa ga abin da yake gaba gare shi, kuma da shiriya da bishãra ga mũminai.
(98) Wanda ya kasance maƙiyi ga Allah da malã'ikunSa da manzanninSa da Jibirĩla da Mĩkã'ĩla to, lalle ne, Allah Maƙiyi ne ga kãfirai.
(99) Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun saukar, zuwa gare ka, ãyõyi bayyanannu, kuma ba wanda yake kãfirta da su fãce fãsikai.
(100) Shin, kuma a kõ da yaushe suka ƙulla wani alkawari sai wani ɓangare daga gare su ya, yi jĩfa da shi? Ã'a, mafi yawansu bã su yin ĩmãni.
(101) Kuma a lõkacin da wani manzo (Muhammadu) daga wurin Allah ya je musu, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da su, sai wani ɓangare daga waɗanda aka bai wa Littãfi, suka yar da Littãfin (Alƙur'ãnin) Allah a bãyan bãyansu, kamar dai sũ ba su sani ba.