(25) Haƙĩƙa, lalle Mun aiko ManzanninMu da hujjõji bayyanannu, kuma Muka saukar da Littãfi da sikẽli tãre da su dõmin mutãne su tsayu da ãdalci, kuma Mun saukar da baƙin ƙarfe, a cikinsa akwai cutarwa mai tsanani da amfãni ga mutãne, kuma dõmin Allah Ya san mai taimakonSa da ManzanninSa a fake. Lalle ne Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi.
(26) Kuma haƙĩƙa, lalle, Mun aiki Nũhu da Ibrahĩm, kuma Muka sanya Annabci da Littĩfi a cikin zuriyarsu; daga cikinsu akwai mai nẽman shiryuwa, kuma mãsu yawa daga cikinsu fasiƙai ne.
(27) Sa'an nan Muka biyar a bãyansu da ManzanninMu; kuma Muka biyar da ĩsã ɗan Maryama, kuma Muka ba shi Linjila kuma Muka sanya tausayi da rahama a cikin zukãtan waɗanda suka bĩ shi, da ruhbãnanci wanda suka ƙãga, shi, ba Mu rubũta shi ba a kansu, fãce dai (Mun rubũta musu nẽman yardar Allah, sa'an nan ba su tsare shi haƙƙin tsarẽwarsa ba, sabõda haka Muka bai wa waɗanda suka yi ĩmãni daga cikinsu sakamakonsu kuma mãsu yawa daga cikinsu fãsiƙai ne.
(28) Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, ku yi ĩmãni da ManzonSa Ya bã ku rabo biyu daga rahamarSa, kuma Ya sanya muku wani haske wanda kuke yin tafiya da shi, kuma Ya gãfarta muku. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai rahama.
(29) Dõmin kada mutãnen Littãfi su san cẽwa lalle bã su da ikon yi ga kõme na falalar Allah, kuma ita falalar ga hannun Allah kawai take, Yanã bãyar da ita ga wanda Ya so (wannan jãhilci yã hana su ĩmani). Kuma Al1ah Mai falala ne mai girma.