البقرة   سورة  : Al-Baqara


سورة Sura   البقرة   Al-Baqara
وَإِذَا طَلَّقْتُمُ النِّسَاءَ فَبَلَغْنَ أَجَلَهُنَّ فَأَمْسِكُوهُنَّ بِمَعْرُوفٍ أَوْ سَرِّحُوهُنَّ بِمَعْرُوفٍ ۚ وَلَا تُمْسِكُوهُنَّ ضِرَارًا لِّتَعْتَدُوا ۚ وَمَن يَفْعَلْ ذَٰلِكَ فَقَدْ ظَلَمَ نَفْسَهُ ۚ وَلَا تَتَّخِذُوا آيَاتِ اللَّهِ هُزُوًا ۚ وَاذْكُرُوا نِعْمَتَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ وَمَا أَنزَلَ عَلَيْكُم مِّنَ الْكِتَابِ وَالْحِكْمَةِ يَعِظُكُم بِهِ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ (231) وَإِذَا طَلَّقْتُمُ النِّسَاءَ فَبَلَغْنَ أَجَلَهُنَّ فَلَا تَعْضُلُوهُنَّ أَن يَنكِحْنَ أَزْوَاجَهُنَّ إِذَا تَرَاضَوْا بَيْنَهُم بِالْمَعْرُوفِ ۗ ذَٰلِكَ يُوعَظُ بِهِ مَن كَانَ مِنكُمْ يُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ ۗ ذَٰلِكُمْ أَزْكَىٰ لَكُمْ وَأَطْهَرُ ۗ وَاللَّهُ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ (232) ۞ وَالْوَالِدَاتُ يُرْضِعْنَ أَوْلَادَهُنَّ حَوْلَيْنِ كَامِلَيْنِ ۖ لِمَنْ أَرَادَ أَن يُتِمَّ الرَّضَاعَةَ ۚ وَعَلَى الْمَوْلُودِ لَهُ رِزْقُهُنَّ وَكِسْوَتُهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ ۚ لَا تُكَلَّفُ نَفْسٌ إِلَّا وُسْعَهَا ۚ لَا تُضَارَّ وَالِدَةٌ بِوَلَدِهَا وَلَا مَوْلُودٌ لَّهُ بِوَلَدِهِ ۚ وَعَلَى الْوَارِثِ مِثْلُ ذَٰلِكَ ۗ فَإِنْ أَرَادَا فِصَالًا عَن تَرَاضٍ مِّنْهُمَا وَتَشَاوُرٍ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْهِمَا ۗ وَإِنْ أَرَدتُّمْ أَن تَسْتَرْضِعُوا أَوْلَادَكُمْ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ إِذَا سَلَّمْتُم مَّا آتَيْتُم بِالْمَعْرُوفِ ۗ وَاتَّقُوا اللَّهَ وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ (233)
الصفحة Page 37
(231) Kuma idan kun saki mãta, sa'an nan suka isa ga ajalinsu (iddarsu), sai ku riƙe su da alhẽri ko ku sallame su da alhẽri, kuma kada ku riƙe su a kan cũtarwa dõmin ta tsawaita idda. Kuma wanda ya aikata wancan, to, haƙĩƙa, yã zãlunci kansa. Kuma kada ku riƙi ãyõyin Allah da izgili. Kuma ku tuna ni'imar Allah da abin da Ya saukar a kanku na Littãfi da hikima. Yana yi muku wa'azi da shi. Kuma ku bi Allah da takawa kuma ku sani cewa lalle ne Allah ga dukan kõme Masani ne.
(232) Kuma idan kuka saki mãta, har suka isa ga ajalinsu (iddarsu), to, kada ku (waliyyansu) hana su, su auri mazansu (da suka sake su) idan sun yarda da jũna a tsakãninsu (tsõhon miji da tsõhuwar mãta) da alhẽri. Wancan ana yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance daga gare ku yana ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Wancan ne mafi mutunci a gare ku, kuma mafi tsarki. Kuma Allah Yana sani, kuma kũ ba ku sani ba.
(233) Kuma mãsu haifuwa (sakakku) suna shãyar da abin haifuwarsu shẽkara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya cika shãyarwa. Kuma ciyar da su da tufãtar da su yana a kan wanda aka haifar masa da alhẽri. Bã a kallafa wa rai fãce iyãwarsa. Bã a cũtar da uwa game da ɗanta, kuma bã a cũtar da uba game da ɗansa, kuma a kan magãji akwai misãlin wancan. To, idan suka yi nufin yãye, a kan yardatayya daga gare su, da shãwartar jũna, to bãbu laifi a kansu. Kuma idan, kun yi nufin ku bãyar da ɗiyanku shãyarwa, to, bãbu laifi a kanku idan kun mĩƙa abin da kukazo da shi bisa al'ãda. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatawa, Mai gani ne.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022