الشعراء   سورة  : Ash-Shu'araa


سورة Sura   الشعراء   Ash-Shu'araa
فَلَمَّا تَرَاءَى الْجَمْعَانِ قَالَ أَصْحَابُ مُوسَىٰ إِنَّا لَمُدْرَكُونَ (61) قَالَ كَلَّا ۖ إِنَّ مَعِيَ رَبِّي سَيَهْدِينِ (62) فَأَوْحَيْنَا إِلَىٰ مُوسَىٰ أَنِ اضْرِب بِّعَصَاكَ الْبَحْرَ ۖ فَانفَلَقَ فَكَانَ كُلُّ فِرْقٍ كَالطَّوْدِ الْعَظِيمِ (63) وَأَزْلَفْنَا ثَمَّ الْآخَرِينَ (64) وَأَنجَيْنَا مُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُ أَجْمَعِينَ (65) ثُمَّ أَغْرَقْنَا الْآخَرِينَ (66) إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ (67) وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ (68) وَاتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ إِبْرَاهِيمَ (69) إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِ مَا تَعْبُدُونَ (70) قَالُوا نَعْبُدُ أَصْنَامًا فَنَظَلُّ لَهَا عَاكِفِينَ (71) قَالَ هَلْ يَسْمَعُونَكُمْ إِذْ تَدْعُونَ (72) أَوْ يَنفَعُونَكُمْ أَوْ يَضُرُّونَ (73) قَالُوا بَلْ وَجَدْنَا آبَاءَنَا كَذَٰلِكَ يَفْعَلُونَ (74) قَالَ أَفَرَأَيْتُم مَّا كُنتُمْ تَعْبُدُونَ (75) أَنتُمْ وَآبَاؤُكُمُ الْأَقْدَمُونَ (76) فَإِنَّهُمْ عَدُوٌّ لِّي إِلَّا رَبَّ الْعَالَمِينَ (77) الَّذِي خَلَقَنِي فَهُوَ يَهْدِينِ (78) وَالَّذِي هُوَ يُطْعِمُنِي وَيَسْقِينِ (79) وَإِذَا مَرِضْتُ فَهُوَ يَشْفِينِ (80) وَالَّذِي يُمِيتُنِي ثُمَّ يُحْيِينِ (81) وَالَّذِي أَطْمَعُ أَن يَغْفِرَ لِي خَطِيئَتِي يَوْمَ الدِّينِ (82) رَبِّ هَبْ لِي حُكْمًا وَأَلْحِقْنِي بِالصَّالِحِينَ (83)
الصفحة Page 370
(61) Sa'an nan a lõkacin da jama'a biyu suka ga jũna, sai abõkan Mũsã suka ce: "Lalle ne mũ haƙĩ ƙa, waɗanda ake riska ne."
(62) Ya ce: "Kayya! Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni."
(63) Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa "Ka dõki tẽku da sandarka." Sai tẽku ta tsãge, kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma.
(64) Kuma Muka kusantar da waɗansu mutãne a can.
(65) Kuma Muka tsĩrar da Mũsã da waɗanda suke tãre da shi gabã ɗaya.
(66) Sa'an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutãnen.
(67) Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
(68) Kuma lalle ne Ubangijinka, kaƙĩƙa, Shĩ ne Mabũwayi, Mai jin ƙai.
(69) Kuma ka karanta, a kansu, lãbãrin Ibrãhĩm.
(70) A sã'ilin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bauta wa?"
(71) Suka ce: "Munã bauta wa gumãka, sabõda haka munã yini mãsu lazimta a gare su."
(72) Ya ce: "Shin, sunã jin ku, a lõkacin da kuke kira?"
(73) "Kõ kuwa sunã amfãnin ku, kõ sunã cũtar ku?"
(74) Suka ce: "Ã'a mun sãmĩ ubanninmu, kamar haka ne suke aikatãwa."
(75) Ya ce: "Shin to, kun ga abin da kuka kasance kunã bautã wa?"
(76) "Kũ da ubanninku mafi daɗẽwa?"
(77) "To lalle ne, sũ maƙiya ne a gare ni, fãce Ubangijin halittu."
(78) "Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yanã shiryar da ni."
(79) "Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni."
(80) "Kuma idan na yi jiyya, to, Shĩ ne Yake warkar da ni."
(81) "Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rãyar da ni."
(82) "Kuma wanda Yake inã kwaɗayin Ya gãfarta mini kurãkuraina, a rãnar sãkamako."
(83) "Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai."
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022