(91) Waɗanda suka sanya Alƙur'ãni tãtsuniyõyi.
(92) To, rantsuwa da Ubangijinka! Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya.
(93) Daga abin da suka kasance sunã aikatãwa.
(94) Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki.
(95) Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu izgili.
(96) Waɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa'an nan da sannu zã su sani.
(97) Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili).
(98) Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada.
(99) Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka.
النحل An-Nahl
(1) Al'amarin Allah yã zo, sabõda haka kada ku nẽmi hanzartãwarsa. Tsarkin Allah ya tabbata, kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka.
(2) Yanã sassaukar da malã'iku da Rũhi daga umurninSaa kan wanda Yake so daga bãyinSa, cẽwa ku yi gargaɗi cẽwa: Lalle ne shĩ, bãbu abin bautãwa fãce Ni, sabõda haka ku bĩ Ni da taƙawa.
(3) Ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya. Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka.
(4) Ya halicci mutum daga maniyyi, sai gã shi yanã mai husũma bayyananniya.
(5) Da dabbõbin ni'ima, Ya halicce su dõminku. A cikinsu akwai abin yin ɗumi da waɗansu amfãnõni, kuma daga gare su kuke ci.
(6) Kuma kunã da kyau a cikinsu a lõkacin da suke kõmõwa daga kĩwo da maraice da lõkacin da suke sakuwã.