هود   سورة  : Hud


سورة Sura   هود   Hud
۞ وَمَا مِن دَابَّةٍ فِي الْأَرْضِ إِلَّا عَلَى اللَّهِ رِزْقُهَا وَيَعْلَمُ مُسْتَقَرَّهَا وَمُسْتَوْدَعَهَا ۚ كُلٌّ فِي كِتَابٍ مُّبِينٍ (6) وَهُوَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ وَكَانَ عَرْشُهُ عَلَى الْمَاءِ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا ۗ وَلَئِن قُلْتَ إِنَّكُم مَّبْعُوثُونَ مِن بَعْدِ الْمَوْتِ لَيَقُولَنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا إِنْ هَٰذَا إِلَّا سِحْرٌ مُّبِينٌ (7) وَلَئِنْ أَخَّرْنَا عَنْهُمُ الْعَذَابَ إِلَىٰ أُمَّةٍ مَّعْدُودَةٍ لَّيَقُولُنَّ مَا يَحْبِسُهُ ۗ أَلَا يَوْمَ يَأْتِيهِمْ لَيْسَ مَصْرُوفًا عَنْهُمْ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُوا بِهِ يَسْتَهْزِئُونَ (8) وَلَئِنْ أَذَقْنَا الْإِنسَانَ مِنَّا رَحْمَةً ثُمَّ نَزَعْنَاهَا مِنْهُ إِنَّهُ لَيَئُوسٌ كَفُورٌ (9) وَلَئِنْ أَذَقْنَاهُ نَعْمَاءَ بَعْدَ ضَرَّاءَ مَسَّتْهُ لَيَقُولَنَّ ذَهَبَ السَّيِّئَاتُ عَنِّي ۚ إِنَّهُ لَفَرِحٌ فَخُورٌ (10) إِلَّا الَّذِينَ صَبَرُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ أُولَٰئِكَ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَأَجْرٌ كَبِيرٌ (11) فَلَعَلَّكَ تَارِكٌ بَعْضَ مَا يُوحَىٰ إِلَيْكَ وَضَائِقٌ بِهِ صَدْرُكَ أَن يَقُولُوا لَوْلَا أُنزِلَ عَلَيْهِ كَنزٌ أَوْ جَاءَ مَعَهُ مَلَكٌ ۚ إِنَّمَا أَنتَ نَذِيرٌ ۚ وَاللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ وَكِيلٌ (12)
الصفحة Page 222
(6) Kuma bãbu wata dabba a cikin ƙasa fãce ga Allah arzikinta yake, kuma Yanã sanin matabbatarta da ma'azarta, duka sunã cikin littãfi bayyananne.
(7) Kuma shi ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwanaki shida, kuma Al'arshinSa ya kasance akan ruwa, dõmin Ya jarrabã ku, wannan ne daga cikinku mafi kyãwon aiki. Kuma haƙĩƙa idan ka ce: "Lalle kũ waɗanda ake tãyarwa ne a bãyan mutuwa," haƙĩƙa waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: "Wannan bai zama ba fãce sihiri bayyananne."
(8) Kuma lalle ne idan Mun jinkirta da azãba gare su zuwa ga wani lõkaci ƙidãyayye, haƙĩƙa sunãcẽwa me yake tsare ta? To, a rãnar da zã ta je musu, ba ta zama abin karkatarwa ba daga gare su. Kuma abin da suka kasance suna yin izgili da shi, yã wajaba a kansu.
(9) Kuma lalle ne idan Mun ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu, sa'an nan kuma Muka zãre ta daga gare shi, lalle ne shĩ, hakĩka, mai yanke tsammãnine, mai yawan kãfrci.
(10) Kuma lalle ne idan Mun ɗanɗana masa ni'ima a bãyan cũta ta shãfe shi, Yana cẽwa mũnanan halaye sun tafi daga wurina. Lalle shi mai farin ciki ne, mai alfahari.
(11) Sai waɗanda suka yi haƙuri kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai. Waɗannan sunã da gãfara da lãda mai girma.
(12) Sabõda haka tsammãninka kai mai barin sãshen abin da aka yi wahayi zuwa gare ka ne, kuma mai ƙuntata ƙirjinka da shi ne dõmin sun ce: "Dõmin me ba a saukar masa da wata taska ba, kõ kuma Malã'ika ya zo tãre de shi?" Kai mai gargaɗi ne kawai. Kuma Allah ne wakili a kan kõme.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022