(246) Shin, ba ka gani ba zuwa ga wasu mashãwarta daga Bani Isrã'ĩla daga bãyan Mũsã, a lõkacinda suka ce ga wani annabi nãsu: "Naɗã mana sarki, mu yi yãƙi a cikin hanyar Allah." Ya ce: "Ashe, akwai tsammãninku idan an wajabta yãƙi a kanku cẽwa bã zã ku yi yãƙin ba?" Suka ce: "Kuma mẽne ne a gare mu, ba zã mu yi yãƙi ba, a cikin hanyar Allah, alhãli kuwa, haƙiƙa, an fitar da mu daga gidãjenmu da ɗiyanmu?" To, a lõkacin da aka wajabta yãƙin a kansu, suka jũya, sai kaɗan daga gare su. Kuma Allah Masani ne ga azzãlumai.
(247) Kuma annabinsu ya ce musu: "Lalle ne, Allah ya naɗa muku ¦ãlũta ya zama sarki." Suka ce: "Yãya ne sarauta zã ta kasance a gare shi, a kanmu, alhãli kuwa mũ ne mafi cancanta da sarauta daga gare shi, kuma ba a bã shi wata wadata ba daga dũkiya?" Ya ce: "Lalle ne, Allah Yã zãɓe shi a kanku, kuma Ya ƙãra masa yalwa a cikin ilmi da jiki. Kuma Allah Yana bãyar da mulkinSa ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadaci ne, Masani.
(248) Kuma annabinsu ya ce musu: "Lalle ne alãmar mulkinSa ita ce akwatin nan ya zo muku, a cikinsa akwai natsuwa daga Ubangijinku da sauran kaya daga abin da Gidan Mũsã da Gidan Hãrũna suka bari malã'iku suna ɗaukarsa. Lalle ne a cikin wancan akwai alãma a gare ku (ta naɗin ¦ãlũta daga Allah ne) idan kun kasance mãsu ĩmãni."