الإخلاص   سورة  : Al-Ikhlaas


سورة Sura   الإخلاص   Al-Ikhlaas
الصفحة Page 604
الإخلاص Al-Ikhlaas
(1) Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci."
(2) "Allah wanda ake nufin Sa da buƙata."
(3) "Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba."
(4) "Kuma babu ɗaya da ya kasance tamka a gare Shi."
الفلق Al-Falaq
(1) Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya"
(2) "Daga sharrin abin da Ya halitta."
(3) "Da sharrin dare, idan ya yi duhu."
(4) "Da sharrin mãtã mãsu tõfi a cikin ƙulle-ƙulle."
(5) "Da sharrin mai hãsada idan ya yi hasada."
الناس An-Naas
(1) Ka ce "Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne."
(2) "Mamallakin mutane."
(3) "Abin bautãwar mutãne."
(4) "Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa."
(5) "Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane."
(6) "Daga aljannu da mutane."
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022